in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya jaddada cewa za a kare manufofin yin hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama
2018-07-10 13:51:55 cri

A jiya ne firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwararsa ta kasar Jamus Madam Angela Dorothea Merkel suka halarci bikin rufe dandalin hadin gwiwar Sin da Jamus karo na 9 ta fuskar kimiyya da fasaha dangane da tattalin arziki da aka yi a birnin Berlin na kasar Jamus, inda Mista Li ya jaddda cewa, ya kamata kasashen biyu su daga matsayin hadin kai dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi, don amfani da wannan mataki da zummar kiyaye manufar daukar mataki a tsakanin bangarori da dama, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Mr Li Keqiang ya bayyana cewa, ya kamata Sin da Jamus su ci gaba da habaka hadin gwiwa ta fuskar ciniki, da kara inganta harkokin ciniki tsakaninsu cikin sauki, da habaka harkokin ba da hidima. Ban da wannan kuma, ya ce, ya kamata bangarorin biyu su kara zubawa juna jari, da shimfida yanayi da makoma mai kyau tsakaninsu cikin adalci, tare kuma da sa kaimi ga hadin gwiwa ta fuskar kirkire-kirkire, da kara bullo da tsare-tsare tare ta fuskar kirkire-kirkire, da kuma yin amfani da dandalin hadin kai a fannin kera motoci masu aiki da wutar lantarki da sana'ar samar da na'urori masu sarrafa kansu da sauransu, ta yadda za a kara hadin kai a sana'o'i na zamani, alal misali na'urori masu sarrafa kansu, motoci dake aiki da makamashi na zamani, da motoci masu sarrafa kansu da sauransu. Ya ce:

"Ba za mu iya yin hasashen saurin bunkasuwar kimiya da fasaha ba, don haka ya kamata mu hada kai da juna don kiyaye 'yancin mallakar fasaha. Ta wannan hanya ce za mu kiyaye muradun masu kirkire-kirkire, ta yadda harkokin kimiya da fasaha za su bunkasa. Ban da wanann kuma, kamata ya yi, mu kara tuntubar juna da yin mu'ammalar fasahohi masu daraja, matakin da zai sa kaimi ga bunkasuwar kimiya, wanda daga bisani zai amfanawa Sin da Jamus har ma ga dukkanin duniya. "

Hakazalika, Mista Li ya jaddada cewa, idan ana son kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Jamus ta fuskokin tattalin arziki da fasahohin zamani, dole ne mu kiyaye yanayin yin cinikayya da zuba jari cikin 'yanci tare da bude kofa ga juna. Hakan ya sa bangarorin biyu sun nanata matsayin da suka dauka na kiyaye tsarin yin ciniki cikin 'yanci da yaki da manufar daukar matakai a kashin kai da manufar ba da kariyar cinikayya, da kuma kiyaye tsarin daukar matakai a tsakanin bangarori daban-daban bisa ka'idoji da dokokin da aka kafa. Ya ce, idan wani ya nace ga tunanin yin watsi da hadin kai wanda bai dace da halin da ake ciki yanzu ba, da tayar da yakin ciniki, matakin zai kawo illa ga moriyar bangarorin biyu da abin ya shafa, har ma ga moriyar kasashe daban-daban a duniya dake da alaka da ita, abin da ba zai kawo amfani ko kadan ba. Ya nuna cewa:

"Kamfanonin Sin da Jamus sun kulla yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu, abin da ba ma kawai ya kawo amfani ga kasashen biyu ba, har ma ya isar da wani sako mai yakini ga duniya da ma al'ummar Turai na cewa, Sin tana kiyaye tsarin daukar mataki a tsakanin bangarori daban-daban, da gudanar da ciniki cikin 'yanci, kuma Sin na daukar matakin da ya dace don nuna cewa, ba za a hana tsarin gudanar da ciniki cikin 'yanci da kafa tsarin tattalin arzikin duniya bai daya ba. Sin da Jamus za su hada gwiwa da sauran kasashe don kiyaye wadannan tsare-tsare."

A nata bangare, madam Merkel ta ce, bangarorin biyu sun sa hannu kan wasu yarjejeniyoyi a fannin kimiya da fasaha, matakan da zai sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakaninsu nan gaba. Jamus da Sin na da makoma mai kyau ta fuskar hadin kai. Kana Jamus na fatan za a samu ci gaba mai armashi a ganawar shugabannin Turai da Sin da za a gudanar, da kuma sa kaimi ga samun sabon ci gaban yarjejeniyar zuba jari tsakanin Turai da Sin, ta yadda za a kare duniya daga shiga dabaibayin manufar ba da kariyar ciniki maras kyau. Ta ce:

"Ina fatan Sin da Jamus za su yi hadin kansu don ba da gudunmawa ga yaki da manufar ba da kariyar ciniki. Ba mu son ganin duniya ta fada cikin dabaibayin wannan mummunar manufa, wannan bai shafi bangarorin biyu ba. Yakin ciniki da aka tayar ya kawo illa ga dukkanin kasashen duniya. Jamus na fatan kara hada kai da Sin don bayyana matsayinmu na goyon bayan ciniki cikin 'yanci da yaki da manufar ba da kariyar ciniki. Kuma ina fatan Jamus da Sin ba ma kawai su hada kai a fannin siyasa ba, har ma su kara hada kai da samun ci gaba mai armashi ta fuskar tattalin arziki a nan gaba."

Rahotanni na cewa, wakilai ta fuskar tattalin arziki fiye da 400 daga bangarorin biyu ne suka halarci dandalin karon nan. (Amina Xu )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China