in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana da karfin mayar da martani ga yakin cinikayyar Amurka
2018-07-10 12:07:46 cri
Tabbas kasar Sin da kasar Amurka dukkansu za su dandana kudar yakin ciniki dake tsakaninsu, babu kasar da za ta yi nasarar wannan yakin. Shi ya sa, tuni kasar Sin ta tsara shirin fuskantar wannan matsala.

A daren jiya ne, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya sanar da matakai guda hudu domin sassauta illolin da rikicin cinikin dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka zai haifar wa kamfanoni da al'umma. Wadanda suka hada da, na farko, nazarin tasirin da yakin zai haifar wa kamfanoni. Sa'an nan kuma, a yi amfani da karin harajin da aka tara wajen sassauta kalubalolin da yakin ya haifar wa kamfanoni da ma'aikatansu. Daga bisani kuma, a sa kaimi ga kamfanonin da su daidaita tsarinsu na shigar da hajoji daga ketare. A karshe, a gaggauta aiwatar da manufofin da gwamnatin kasar Sin ta fitar na yin amfani da jarin da kamfanonin ketare suka zuba yadda ya kamata, inganta bunkasuwar tattalin arziki mai inganci, kara aikin kare 'yancin kamfanoni bisa doka da kuma kyautata yanayin zuba jari a kasar Sin da dai sauransu.

Kamar yadda wasu masana suka ce, kara harajin kwastan kan hajojin kasar Sin da darajarsu ta kai dallar Amurka biliyan 34 da kasar Amurka ta yi, zai haddasa babbar matsala ga kamfanonin kasar Sin da abin ya shafa, har ma ga rayuwar ma'aikatan wadannan kamfanonin. Gwamnatin kasar Sin ta san da hakan, shi ya sa, ba ta son tayar da yakin ciniki tun farko. Amma, babu sauran hanyar da za ta iya zaba, sai dai kasar Sin ta mayar da martani ga yakin cinikayya da kasar Amurka ta tayar da shi.

Matakai biyu na gaba daga cikinsu da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta dauka domin taimaka wa kamfanonin da abin ya shafa kai tsaye. Sa'an nan, mataki na uku da ta dauka ya sa kaimi ga kamfanonin da su kara shigo da hajoji daga sauran kasashe da yankuna. A karshe, ta fidda wannan mataki na hudu, inda take mai da hankali wajen kyautata tsarin raya tattalin arziki da kuma kare kamfanonin kasar Sin, ta yadda za a sassauta matsalolin da yakin cinikin zai haifar musu.

Haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da daidaita manufofinta domin fuskantar matsalolin da yakin cinikin zai haifar wa kasar.

A yayin da take tinkarar yakin ciniki da kasar Amurka ta tayar, ko kasar Sin za ta iya jure asarar da za ta yi? Za a iya ganin cewa, kasar Sin ita ce kasa daya tak a duniya wadda ta mallaki dukkan nau'ikan masana'antu daban daban, sa'an nan kasuwar cikin gidanta tana da girma wadda ta kunshi al'ummar da yawansu ya kai biliyan 1.4. Hakan na nufin, ko da yanayin cinikin duniya ya shiga wani hali mafi tsanani, kasar Sin za ta iya gudanar da ayyukan tattalin arziki cikin gida ba tare da dogaro kan wani ba. A sa'i daya kuma, ana iya ganin cewa, kashi 91% daga cikin karuwar tattalin arzikin kasar Sin an same su ne bisa biyan bukatun kasuwannin cikin gida. Kana kashi 60 cikin dari na biyan bukatun cikin gidan kasar Sin sun kasance bukatun jama'ar kasar na sayen kayayyaki da hidimomi, wanda har yanzu yana ta karuwa. Sa'an nan abun da ya fi muhimmanci shi ne, yawan kamfanonin masu kirkiro sabbin fasahohi da kasar Sin ke da su ya kai matsayi na biyu a duniya, inda manufar kasar ta fannin raya kasa ta sabbin fasahohi ta sa tattalin arzikin kasar ya kara zama mai juriya.

Yadda ake kokarin tinkarar yakin cinikin da kasar Amurka ta tayar ya zama yakin da ake yi don tabbatar da makomar kasa ga kasar Sin. Mun san cewa kasar Sin tana da dimbin tarihi na tsawon fiye da shekaru dubu 5. Wannan tarihi, da al'adun da tarihin ya haifar, sun baiwa Sinawa wani ra'ayi na kare muradun kasa. Yayin da ake fuskantar wannan yaki na neman tabbatar da makomar kasa, Sinawa sun fahimci cewa, idan babu muradun kasa, ba za a iya tabbatar da muradun daidaikun mutane ba. Don haka Sinawa za su yarda da jure asarar da ka iya faruwa a fannin zaman rayuwarsu, sa'an nan su yi kokari tare da gwamnatinsu mai daukar nauyin tinkarar kalubaloli, da kokarin kiyaye ci gaban tattalin arzki mai dorewa, da makomar al'umma mai haske. Wannan, a hakika, shi ne ainihin karfin da kasar Sin ke da shi wajen tinkarar yakin cinikin da kasar Amurka ta tayar. (Bello Wang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China