in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da sabon mataimakin shugaban kasa da Ministoci 8 a Gambia
2018-07-10 09:41:10 cri
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow, ya jagoranci bikin rantsar da sabon mataimakinsa Ousainou Darboe tare da wasu ministoci 8 a fadar gwamnati dake birnin Banjul.

Sabbin ministocin sun hada da: na yada labarai da kayakin more rayuwa, da na kudi da harkokin tattalin arziki, da na aikin gona, da na harkokin waje, da minista mai kula da filaye da gwamnatin yankuna, da na cinikayya, sai na matasa da wasanni da kuma na lafiya da walwalar jama'a.

A jawabinsa, shugaba Adama Barrow, ya ce sabuwar Gambia na bukatar su bi kyakkyawar hanyar hidimtawa kasa. Ya ce la'akari da kalubalen da suke fuskanta, ba zai yiwuwa kasar ta rika tafiyar hawainiya ba, maimakon hakan, kamata ya yi su yunkura tare cikin kuzari da himma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China