in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yakin cinikayya zai matsawa kamfanonin kasar Amurka lamba
2018-07-09 13:46:07 cri

Tun daga Jumma'ar da ta gabata, kasar Amurka ta fara karbar karin harajin kwastam da ya kai kashi 25% kan kayayyakin da ake shigar dasu wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 34 daga kasar Sin zuwa cikin kasar Amurka, lamarin da ya haifar da matsin lamba sosai ga kamfanonin kasar Amurka.

Game da manufar karbar karin harajin da kasar Amurka ta dauka, Ralph Ives, mataimakin babban darekta mai kula da nazarin tsare-tsaren duniya na hadaddiyar kungiyar fasahohin aikin jinya masu ci gaba ta kasar Amurka, ya bayyana damuwarsa, inda ya ce,

"Matakin da aka dauka ya shafi kayayyakin da muke shigo da su, wanda zai haifar da matsin lamba ga kamfanoni masu hada kaya na kasar Amurka. Domin za a kara kashe kudi wajen sayen kayayyakin da ake bukata, kuma ba za a biya musu diyya ba. "

Cikin jerin sunayen kayayyakin da aka kara harajinsu akwai wasu na'urorin aikin jinya. Dangane da batun, mista Ives ya fadawa wakilin CRI cewa, gwamnatin kasar Amurka ta ce tana fatan kara kwarewar kamfanonin kasar Amurka wajen takara da takwarorinsu na kasashe daban daban, amma a hakika matakin da aka dauka ya shafi kara harajin da ake karba kan wasu kayayyakin da ake shigar da su, abin da ya yi matsin lamba ga kamfanonin kasar Amurka. Daga bisani, kamfanonin kasar za su rasa damar takara da sauran kamfanoni na wasu kasashe.

Sa'an nan a nata bangare, cibiyar nazarin tattalin arzikin duniya ta PIIE ta kasar Amurka ta sanar da wani rahoto a kwanakin baya, inda aka nuna cewa, dalilin da ya sa gwamnatin Trump ta dauki matakin kara karbar haraji shine, domin tsoron ganin kasar Sin ta samu ci gaba a fannin kimiyya da fasaha. Sai dai burinta na gurgunta kasar Sin ba zai cika ba, maimakon haka matakin data dauka zai haifar da illa ga tsarin samar da kaya da ya shafi kasashe daban daban, da kuma matsawa kamfanonin kasar Amurka lamba. Mai nazarin ilimin tattalin arziki, wadda ta taimaka wajen rubuta wannan rahoto, Madam Mary Lovely, ta ce wadanda za su fi shan wahalar matakin karin haraji ba kamfanonin kasar Sin bane. A cewarta,

"Akasin haka, kamfanonin da za su fi shan wahalar wannan mataki su ne na kasashen Amurka, Japan, da kuma na nahiyar Turai, wadanda suke sarrafa kayayyaki a kasar Sin, sa'an nan su sayar da su zuwa kasuwannin kasar Amurka. "

A nasa bangare, Chad Bown, shi ma wani masanin ilimin tattalin arziki ne na cibiyar nazari ta PIIE, ya ce mafi yawa daga cikin kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su, manyan kamfanonin kasa da kasa ne ke hada su a kasar Sin. A cewarsa,

"Musamman ma a fannonin da suka shafi kwamfuta da na'urorin lantarki, kusan kashi 87% na kayayyakin da kasar Amurka ke shigo da su ba na kamfanonin kasar Sin ba ne. Kayayyakin da wasu manyan kamfanoni na kasashen Amurka, Japan, Koriya ta Kudu, da Turai suke samarwa ne, ba kayayyakin da kamfanonin kasar Sin ke samar dasu ba ne. Don haka matakin kara karbar harajin nan na da ban mamaki. A hakika zai lahanta kamfanoni na sauran kasashe, musamman ma rassan kamfanonin kasar Amurka, da kamfanonin kawayen kasar Amurka."

Masu nazarin al'amuran tattalin arziki sun ce, yawancin kayayyakin da aka shigar dasu cikin kasar Amurka ba kayayyakin da za a sayar da su kai tsaye ba ne. Maimakon haka, za a kara sarrafa su cikin ma'aikatun kasar Amurka, sa'an nan a sayar da su a matsayin kayayyakin kirar kasar Amurka. Saboada haka, matakin da kasar Amurka ta dauka na kara karbar haraji bisa wadannan kayayyaki a hakika yana karawa kamfanonin kasar Amurka nauyi, da lahanta moriyarsu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China