Tashar talabijin ta CNNTurk ta bada rahoton cewa, biyar daga cikin taragun jirgin shida ne suka kauce hanyar da yammacin jiya a lardin Tekirdag, a lokacin da jirgin kasan ke dauke da fasinjoji kimanin 360.
Gwamnan lardin Tekirdag, Mehmet Ceylan yace, mamakon ruwan sama wanda ya haddasa zaftarewar kasa ne ya haifar da kaucewar hanyar jirgin kasan.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Demiroren, jirgin kasan yana kan hanyarsa ne ta zuwa Istanbul wanda ya taso daga lardin Edirne dake kusa da kan iyakar kasar Turkiyya da Bulgaria.
Rahotannin sun ce, tuni aka tura tagawar jami'an ceto da motocin daukar marasa lafiya da jiragen sama masu daukar marasa lafiya zuwa inda hadarin ya auku.