in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Kasa da kasa sun ki amincewa da yakin ciniki da kasar Amurka ta tada
2018-07-07 20:36:34 cri
Amurka ta fara amfani da karin harajin da ta yi da kaso 25 cikin 100 kan kayayyakin kasar Sin da ake shigarsu kasar Amurka a jiya Juma'a, inda ta tada yakin ciniki mafi girma a tarihin dan Adam a fannin tattalin arziki, abun da kuma kasa da kasa suka ki amincewa da shi. Masana da jami'ai da kafofin watsa labaru na kasa da kasa, sun gabatar da ra'ayoyinsu tare da yin Allah wadai da manufofin ciniki da gwamnatin Trump ta kasar Amurka ta gabatar tare da nuna damuwa ga sakamakon da za a samu a nan gaba, kana sun yi nuni da cewa, manufar Trump ta maida kasar Amurka zama matsayin farko ba za ta cimma nasara ba.

"Yakin cinikin ya yi kama da rikicin hada-hadar kudi na duniya da ya faru a shekarar 2008"

Direktan cibiyar binciken manufofin Sin ta kasar Spaniya Xulio Rios, ya bayyana a jiya cewa, burin yakin ciniki da kasar Amurka ta tada shi ne, samar mata moriya mafi girma, da tabbatar da matsayinta na kama karya a duniya don tinkarar bunkasuwar kasar Sin. A cewarsa, watakila bayan wasu makwanni, tasirin da za a samu zai kai kayayyakin da darajarsu za ta kai dala biliyan 1000, da haifar da hasara ga yawan ciniki a duniya da kashi 6 cikin dari da kuma yawan cinikin waje na kasar Amurka da kashi 25 cikin dari, hakan zai yi illa ga dangantakar dake tsakanin kasa da kasa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, tare da bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa, kuma mai yiwuwa sauran kasashe su bi sahun Amurka na yin amfani da harajin kwastam a matsayin makamin ba kan su kariya. Ya jaddada cewa, yakin ciniki na wannan karon ya yi kama da rikicin hada-hadar kudi na duniya da aka fara samu a Amurka a shekarar 2008, wanda kasashen duniya suka nuna damuwa a kai.

A nashi bangare, shugaban majalisar wakilai ta kasar Belgium, Siegfried Bracke, ya fadawa wakilin CRI cewa, dalilin da ya sa gwamnatin Trump ta tayar da yakin ciniki shi ne, cika alkawarin da ya yi yayin takarar neman zabe. Sai dai a ganin mista Bracke, karin harajin kwastam daga wata kasa kan wata bisa radin kai, ya sabawa ka'idar ciniki cikin 'yanci. Saboda haka, idan an ci gaba da mai da hankali kan yanayin da ake ciki, za a ga yadda manufar mai da Amurka gaban sauran kasashe da Donald Trump ya tsaya a kai za ta ci tura.

Ban da haka kuma, jaridar Financial Time ta kasar Birtaniya ta watsa labarin cewa, shugaban baitulmalin kasar Birtaniya ya riga ya gargadi kasashen duniya, inda ya ce wani babban yakin ciniki ka iya hana karuwar tattalin arzikin duniya. Masu nazarin ilimin harkar kudi na kasar sun sheda cewa, idan harajin kwastam da ake karba bisa cinikin da ake yi tsakanin kasar Amurka da manyan abokan cinikayyarta ya karu da kaso 10, to irin tasirin da ake samu a fannin ciniki kawai zai sa jimillar kayayyakin da ake samarwa ta ragu da 2.5% a kasar Amurka, da kuma kashi 1% a duk duniya. Idan lamarin ya girgiza imanin da ake da shi kan yanayin kasuwanci na duniya, da sanya kaddamar da manufar tsumulmula a harkar kudi, to, ba za a samu damar soke harajin da aka kara ba, lamarin da zai sa a ci gaba da rage samar da kayayyaki.

"Kasar Amurka za ta yi asara fiye da ta kasar Sin"

Kamfanin watsa labarai na BBC ya yi tsokacin cewa, yayin da ake yakin ciniki a tsakanin Sin da Amurka, tattalin arzikin kasashen 2 za su fuskanci hadura mafi yawa. Sai dai ba kasashen 2 kawai hadarin zai shafa ba. Taimur Baig, manazarcin ilimin tattalin arziki na kamfanin DBS, ya ce babban yakin ciniki ka iya haddasa raguwar jimilar ma'aunin tattalin arziki na GDP da ta kai kashi 0.25% ga kasashen Sin da Amurka. Ya kara da cewa, la'akari da yadda karuwar tattalin arzikin Sin a shekara ke kai wa kashi 6 zuwa 7 bisa dari, yayin da ta Amurka ke kai wa kashi 2 zuwa 3 bisa dari, ana hasashen cewa asarar da kasar Amurka za ta samu za ta wuce ta kasar Sin. Ban da haka kuma, saboda yakin cinikin zai kawo illa ga tsare-tsaren samar da kayayyaki masu alaka da yankuna daban daban, da haifar da illa ga tattalin arzikin kasashen Koriya ta Kudu, da Singapore, da yankin Taiwan na kasar Sin, da dai sauransu, daga karshe dai, jama'ar kasar Amurka za su ware karin kudi wajen sayen kayayyakin da suke bukata.

Bisa wani rahoton da jaridar New Zurich Daily ta bayar, an ce, Donald Trump bai bude sabuwar kasuwa ta hanyar yin aikin diflomasiyya a fannin cinikayya ba, amma ya amince da matakin da ma'aikatan gwamnatinsa dake Washington suka dauka, irin na bunkasa tattalin arziki bisa shiri kawai. Bai ambaci ko kalma guda kan kayayyakin more rayuwar jama'a ko ayyukan ba da ilmi da dai sauran kayayyakin da suke daidai da bukatun jama'a ba. Ya zuwa yanzu kasar Amurka ba ta samu ci gaba ba, illa hadarin koma baya da take fuskanta.

"Yin kokarin neman samun karin abokan cinikayya, ta yadda bunkasuwar tattalin arziki da cinikayya a duk duniya za ta kai wani sabon matsayi"

A ganin Xulio Rios, direktan cibiyar Spaniya ta yin bincike kan manufofin kasar Sin, ga sauran kasashen duniya, mataki mafi dacewa da za su dauka yanzu shi ne, kokarin neman samun karin abokan cinikayya domin rarraba hadarurrukan dake kasancewa a gabansu, musamman ya kamata su karfafa matsaya daya da suka cimma kan harkokin mulkin duk duniya, domin tinkarar manufofin kafa shinge ga cinikayyar da ake yi tsakanin kasa da kasa, da matakin mai da wani saniyar ware. An yi hasashen cewa, nahiyar Turai ko sauran muhimman kungiyoyin tattalin arziki, amma ban da kasar Amurka, za su kara yin ma'amala tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya. Hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake kasancewa tsakanin kasashen Sin da Turai da Japan da sauran muhimman kungiyoyin tattalin arzikin duniya ta fi muhimmanci. Nan da wasu shekaru masu zuwa, idan matakin mai da wani saniyar ware ya tsananta, kasar Amurka za ta nisanta kanta daga kasuwannin tattalin arziki da cinikayya na duk duniya, amma huldar dake tsakanin sauran muhimman kungiyoyin tattalin arziki za ta karfafu, har ma bunkasuwar tattalin arziki da cinikayya a duk duniya za ta kai wani sabon matsayi.

Manazarta sun bayyana cewa, yanzu a kasar Amurka, dalillin da ya sa darajar kudinta wato Dala, ko sana'o'inta na kimiyya da fasaha ke da karfi sosai a duk duniya shi ne dogaro da goyon bayan kasar Sin wadda take da wata kasaitacciyar kasuwa da dimbin 'yan kwadago masu arha. Wannan dalili ne ya sa kasar Amurka ta hau kan matsayin farko a duk duniya. Idan tana son yin yakin cinikayya ba tare da kasala ba, shi ke nan, sai a dakatar da samar mata arziki, idan babu arziki, tabbas za ta sha kaye. A daya bangaren, manufar cinikayya da ta dauka yanzu ta fusata duniya, tabbas dukkan kasashen duniya za su mayar da Amurka wadda ke matsayin farko yanzu saniyar ware. (Sanusi/Zainab/Bello)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China