in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayin mamaye harkokin cinikayyar duniya da Amurka ke dauka ba zai yi nasara ba
2018-07-06 21:03:53 cri


Yau Juma'a, kasar Amurka ta soma kara karbar harajin kashi 25 cikin 100 kan kayayyakin da aka shigo da su daga kasar Sin da darajarsu ta kai dalar biliyan 34. Domin mayar da martani, a wannan rana kasar Sin ita ma ta kara karbar haraji na kashi 25 cikin 100 kan kayayyakin cinikayya da aka shigo da su daga Amurka da darajarsu ta kai dalar biliyan 34.

A jawabinsa kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar Sin ya bayyana cewa, an tilastawa kasar Sin daukar wannan martani ne don kare muradunta da na jama'arta. Wannan ya nuna cewa, an soma yakin cinikayya mafi girma a tarihin tattalin arzikin 'dan Adam.

Ko shakka babu, ba kasar Sin ita kadai ke yaki da Amurka ba. Kafin haka, kungiyar EU, Canada, Mexico, India da Turkiya da sauransu sun soma yakin cinikayya don mayar wa Amurka martani. A yanzu haka, karfin yaki da ra'ayin mamaye harkokin cinikayya da Amurka ke dauka na karuwa a duk fadin duniya.

A matsayinta na kasa mafi karfi a duniya, kasar Amurka tana da fifiko a fannonin tattalin arziki, kimiyya da fasaha, aikin soja da dai sauransu. A baya ma, ta bullo da ra'ayin neman mallakar duniya, inda ta dauki kanta a matsayin 'yar sandan duniya". Amma, yanzu ta yi watsi da wancan manufa, tana daukar kanta a matsayin wadda ta fi kowa a duniya, tana amfani da batun karbar haraji don raya ra'ayinta na mamaye harkokin cinikayya a duniya. Hakan ba kawai zai hana farfadowar tattalin arziki duniya da jawo tashin hankali a kasuwannin duniya ba, har ma zai kawo illa ga muradun kamfanoni da masu sayen kayayyaki, ciki har da kamfanoni da jama'ar Amurka. A hakika, a cikin takardar jerin sunayen kayayyakin cinikayyar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 34 da Amurka ta sanar game da kara karbar haraji, kashi 59 cikin 100 kayayyaki ne da kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin ke fitarwa, ciki har da wasu kamfanonin Amurka. Ana iya cewa, a yayin da Amurka ke jefa duniya cikin halaka, a sa'i daya tana kokarin janyo ruwan dafa kanta da kanta. Don haka, tun da farko ana iya tabbatar da cewa makomar ra'ayin mamaye harkokin cinikayya ba zai yi nasara ba.

Da farko, idan aka waiwayi yake-yaken cinikayya da kasar Amurka ta tayar, duk domin a bullo da matsaloli a harkokin tattalin arzikinta. Masu mulkin kasar sun yi haka ne da nufin shafawa wasu kasashen ketare kashin kaji ta hanyar tayar da yakin cinikayya. Amma, sakamakon cewa, wannan mataki ba zai warware matsalolin Amurka ba, har ma ya jawo tabarbarewar tattalin arzikin duniya.

Na biyu, kamar yadda Sinawa kan ce, idan ka tsaya kan gaskiya, jama'a suna tare da kai, amma idan ba ka tsaya kan gaskiya ba, jama'a za su rabu da kai. Yakin cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ba ma kawai takara ce da ake tsakanin manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya ba, takara ce da ake yi tsakanin kasar da ta nuna fin karfi da kasar da ta mutunta doka da oda, kana takara ce da ake yi tsakanin kasar dake bin ra'ayin bada kariya ga cinikayya da kasar dake bin ra'ayin yin cinikayya ba tare da kafa shinge ba. Sin kasa ce dake nuna goyon-baya ga gudanar da cinikayya cikin 'yanci da kuma tsarin yin cinikayya dake kunshe da bangarori daban-daban, haka kuma ta fitar da ra'ayin raya makomar bil'adama ta bai daya, da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", kana tana maraba da kasashe daban-daban da su yi amfani da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya kasa, al'amarin da ya samu maraba sosai daga kasashe daban-daban. Amma irin abubuwan da kasar Amurka ta yi na nuna son kai sun gamu da suka daga kasashen duniya.

Na uku, a cikin kasar Amurka, akwai mutane da dama wadanda suka nuna adawa ko rashin amincewa da yakin cinikayya da gwamnatin Trump ta kaddamar kan kasar Sin. Jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta ce, kaddamar da yakin cinikayya, caca ce ta fannin tattalin arziki mai cike da hadari da gwamnatin Trump ta yi. Kuma a halin yanzu, gwamnatin Trump na kara fuskantar hadari na rashin samun nasara a cacar, kuma mamaye harkokin cinikayya da Amurka ta yi ya gamu da babbar adawa a cikin kasar.

Na hudu, kasar Sin na da tushe mai inganci da karfi sosai wajen tinkarar kalubalen tattalin arziki. A halin yanzu, kasar Sin na kara bude kofa ga kasashen waje, da kara samar da alheri ga jama'ar kasar da na fadin duniya, a wani mataki na sanya sabon kuzari wajen samun galaba cikin yakin cinikayyar da Amurka.

Tarihi ba zai manta da ranar 6 ga watan Yulin shekara ta 2018 ba, inda Amurka ta tada rikicin cinikayya mafi girma a tarihi. Ya zama dole kasashen duniya su zama tsintsiya madaurinki daya, da kare tsarin cinikayya cikin 'yanci, don samun galaba kan mamaye harkokin cinikayya da Amurka ke kokarin yi. (Bilkisu, Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China