in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron manema labaru kan halartar Xi Jinping bikin bude taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Kasashen Larabawa
2018-07-06 13:53:34 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira wani taron manema labarai a yau, inda mai ba da taimako ga ministan harkokin waje Mista Chen Xiaodong ya yi bayani kan halartar bikin bude taron ministocin karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Larabawa da shugaban Sin Xi jinping zai yi.

Chen Xiaodong ya ce, shugaba Xi Jinping zai halarci bikin bude taron gobe da yin jawabi, tare da Sheikh Sabah Al Ahmad AlJaber Al-Sabah na Kuwait, wanda zai kawo ziyarar aiki a Sin, da wasu ministoci 21 daga kasashen Larabawa da babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa. Wannan ne karo na 3 da shugaba Xi ya gabatarwa kasashen Larabawa manyan manufofin da Sin ke dauka, matakin da ya bayyana cewa, Sin tana goyon baya da kuma dora muhimmanci sosai ga bunkasuwar dangantakar Sin da kasashen Larabawa da raya wannan dandali, lamarin dake da ma'ana mai yakini cikin dogon lokaci. Wato daga matsayin dangantakar bangarorin biyu zuwa sabon matsayi, da ciyar da shawarar "ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar gaba, har ma da taka rawa ga samar da zaman lafiya da bunkasuwar yankin gabas ta tsakiya cikin lumana. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China