in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta tada rikicin cinikayya mafi girma a tarihi
2018-07-06 13:48:49 cri
Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce Amurka ta ta da rikicin cinikayya mafi girma a tarihi, la'akari da karin haraji da ta yi, da kaso 25 kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 34, wanda zai fara aiki a yau Juma'a, Kakakin ma'aikatar ta kasar Sin ya bayyana cewa, matakin na Amurka ya take dokokin hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, kuma alama ce ta nuna fin karfi, wanda kuma ke barazana da tsaron ayyukan bangaren ciniki da masana'atu. Bugu da kari, zai tsananta farfadowar tattalin arzikin duniya da haifar da matsala ga kasuwar duniya tare da yin illa ga jama'ar dake sayen kayyaki da kasa da kasa da kuma kamfanoni. A cewar ma'aikatar ta kasar Sin, matakin illa kawai zai yi, maimakon kare moriyar kamfanoni da al'ummar Amurka. Ta kara da cewa, an tilastawa kasar Sin wadda ta lashi takobin ba za ta tada rikicin cinikayya ba, mayar da martani, domin kare moriyar kasa da al'ummarta, Kasar Sin za ta gabatar da yanayin da ake ciki ga hukumar WTO, sannan za ta tsaya tare da sauran kasashen duniya wajen kare tsarin cinikayya cikin 'yanci tsakanin kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China