in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin hadin gwiwar watsa labarai na Sin da Rwanda ya yi kira da a kara zurfafa hadin kai
2018-07-06 11:13:12 cri

Wakilai daga kafofin watsa labarun Sin da na kasar Rwanda sama da 100, sun gudanar da dandalin hadin gwiwa, domin bunkasa musaya, da kuma ci gaba da inganta hadin kai.

Yayin taron na jiya Alhamis, mataimakin jagoran ofishin yada bayanai na majalissar zartaswar kasar Sin ko SCIO a takaice Guo Weimin, ya ce dandalin na da nufin samar da wata kafa ta musayar bayanai da tsare tsare, wadda za su habaka rawar da kafafen watsa labarai ke takawa, wajen wayar da kai, da fadada kawance, da abuta tsakanin al'ummun kasashen biyu, ta hanyar tattaunawa, da aiwatar da wasu shirye-shirye na musamman.

Yayin da mahalarta dandalin ke tafka muhawara, sun bayyana aniyar su, ta zakulo hanyoyin samar da ci gaba cikin hanzari a wannan fanni, a gabar da kafafen watsa labarai ke kara fuskantar kalubale iri iri daga kafafen sada zumunta na zamani da kuma sabbin fasahohi.

Mahalarta taron sun kuma amince da muhimmancin da karfafa hadin gwiwa, da musaya ke da su, wajen yada sahihan bayanai da al'umma za su amfana daga gare su. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China