in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kauyen Liang-Jia-He(6)
2018-07-06 11:13:27 cri

Ga babi na shida

Manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare ta sanya mazauna kauyen Liang-Jia-He suke zaman jin dadi.

Liu Ruilian ta sha wahala sosai a lokacin da take karama. A tunaninta, ita da 'yan uwanta su hudu ba su taba sanya takalma ba a yanayin zafi, kuma suna sanya babban bargo na zamani guda kawai da dare, a lokacin kuma da kyar suke iya cin turararren burodi.

A lokacin da take da shekaru 17 da haihuwa, Liu Ruilian ta auri Gong Zhengfu na kauyen Liang-Jia-He, amma sun yi ta shan wahalar zaman rayuwa bayan auren.

Bayan Xi Jinping ya kama aikin sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na Liang-Jia-He, ya kafa kungiyar sana'ar sarrafa karfe, da kantin sayar da kaya, da kungiyar madinka daya bayan daya. Kungiyar madinkan ta bukaci 'yan kungiyar mata guda uku, ba zato ba tsammani an zabi Liu Ruilian da ta zama wata mambar kungiyar, har ta kasa yin barci a duk tsawon dare saboda farin ciki.

Kungiyar madinkan ta gudanar da tsarin neman makin aiki ne bisa yawan kayayyakin da aka dinka. Domin kokarin samun makin aiki da yawa, Liu Ruilian ta tattauna da mijinta Gong Zhengfu, sun yi bashin kudi don sayen wata na'urar dinki. Kullum tana dinka kayayyaki bayan cin abinci kadan, kuma ta kan dawo da kayayyaki zuwa gida don ci gaba da aikin.

A lokacin bazara a shekarar 1984, a karon farko Liu Ruilian ta ji an ce an yarda da a aiwatar da manufar tabbatar da yawan amfanin gona da kowane iyali ya samar wa gwamnati. A lokacin, ba ta san amfanin wannan manufa ga zaman rayuwarta ba, har ma ba ta sani ba, an riga an soma yin gyare-gyare duk fadin yankunan karkarar kasar Sin.

Kamar yadda sauran manoman arewacin lardin Shaanxi suke, iyalin Liu Ruilian sun soma yin zaman rayuwa mai dadi sakamakon kokarin da suka yi. Koda yake ba su rasa abinci ba, amma ba su da isassun kudade. Da ta ga wasu mazauna da suka tafi birane don cin rani, sai Liu Ruilian ita ma take fatan neman aikin yi a birane. A lokacin da babu aikin gona, ita da mijinta sun tafi garin Yanchuan don yin aiki, sannu a hankali zaman rayuwarsu na samun kyautatuwa. An kira wadancan mazaunan dake neman aikin yi a birane na "manoma 'yan cin rani na farko" na Liang-Jia-He. Aikin yin gyare-gyare ya kawo sauye-sauye ga kauyuka da ba a taba gani ba a da. Sannan aikin bude kofa ga ketare ma ya samar da wata kyakkyaar makoma ga irin wadannan sauye-sauyen.

A shekarar 1993, Xi Jinping wanda ya kama aikin sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na birnin Fuzhou, ya dawo Liang-Jia-He, da ganin mazauna kauyen ba za su damu kan zaman rayuwarsu ba, ya yi farin ciki sosai. Cin abinci har a koshi ya taba kasancewar wani buri ne na Xi Jinping da mazauna kauyen, yanzu duk iyalan kauyen suna da isassun hatsi, ba shakka ya yi farin ciki sosai.

Shekarar 1999, ta kasance shekarar da tattalin arziki da yanayin zaman rayuwar al'ummar yankin Yan'an ta soma samun ci gaba sosai. Bisa manufar mayar da gonakin dake kan dutse mai gangare su koma gandun daji, Yan'an ya mayar da dukkan yankuna masu tudu da gangare da su zama gandun daji, hakan aka soma yin kwaskwarima na tsimin makamashi cikin sauri a duk birnin.

Tun baya da aka fara mayar da yankuna masu tudu da gangare da su zama gandun daji a shekarar 1999, fadinsu ya zarce kadada dubu 660, hakan ya sa an sake ganin bishiyoyi masu launin kore a yankunan birnin Yan'an.

A ranar 28 ga watan Agusta na shekarar 2007, Xi Jinping ya rubuta wasika ga mazauna kauyen, inda ya bayyana cewa, ya yi matukar farin ciki da samun labarin kan cewa, an samu yawan bishiyoyi da ruwa mai tsabta a Liang-Jia-He. Kana ya karfafa zukatan mazauna kauyen da su yi imanin cewa, zamansu zai kara samun kyautatuwa bisa kokarin da suka yi a inuwar manufofin kawowa jama'a alheri na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma ayyukan da reshen jam'iyyar dake kauyen da kwamitin kula da harkokin kauyen suka gudanar.

A watan Yuli na shekarar 2013, an yi mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Yan'an, wanda aka shafe tsawon kwanakin ana yin ruwan mai karfin wanda aka rabon yankin da a yi ruwan sama mai tsanani irinsa tun bayan shekarar 1945. Hadarin ya addabi mutane kimanin miliyan 1.5 na gundumomi 13 da ke yankin, yawan hasarar kudi da aka samu kuwa ya kai fiye da RMB Yuan biliyan 12. Haka kuma a cikin wannan bala'i mai tsanani, an lalata gidajen kogon dutse kashi 80 cikin dari na manoman kauyen Liang-Jia-He, har ma wasu sun rushe.

Yayin da ake aikin sake ginawa, gwamnatin wurin ta tsayar da kudurin kaurar da dukkan mazauna kauyen Liang-Jia-He, wato gidaje fiye da 100 na kauyen za su koma sabbin matsugunai a garin Wen An Yi, yaran kauyen ma za su samu damar yin karatu a garin. Tsohon kauyen kuwa bayan sake gina shi, za a mayar da shi a matsayin wurin horo ga 'yan jam'iyyar da matasa, da ma wurin ba da misali a matsayin wani kyakkyawan kauye.

A watan Janairun shekarar 2014, kwamitin kula da harkokin kauyen Liang-Jia-He ya rubuta wasika ga Shugaba Xi Jinping, inda aka bayyana yadda ake raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kauyen da kuma aikin sake gina kauyen. Shugaba Xi ya amsa wasikar a ranar 5 ga watan Mayu, inda ya ce,

"A lokacin zafi na bara, an gamu da hadarin ruwa mai tsanani a yankin Yanchuan, kullum na kan damu da 'yan uwana da ke kauyen. Daga baya na yi farin ciki sosai da samun labarin cewa, bisa goyon bayan jam'iyya da gwamnati, kun jagoranci mazauna kauyen wajen tunkarar bala'in, da sake gina kauyen, har ma da raya aikin gona yadda ya kamata, lamarin da ya sa yawan kudin shiga da mazauna kauyen suka samu ya sake karuwa. Kauyen ya tsara sabon shirin bunkasuwa a bana, ina fatan za ku kara yin kokari tare da mazauna kauyen domin kara kyautatuwar zamanku da kuma kayatar kauyenmu."

Liu Jinlian, wadda ta taba baiwa Xi Jinping dakin kwana yayin da yake zama a kauyen Liang-Jia-He, ta ce, za ta je ganin likita ba tare da bata lokaci ba, idan ta kamu da cuta. A farkon tsakiyar shekarar 2015, Liu Jinlian ta ji ciwo a wani hannunta. Bayan an yi mata bincike a asibiti, an gano wani kari, sa'an nan an yi mata tiyata. Liu Jinlian ta ce, an mayar mata da kudi kusan RMB Yuan 8000 da ta kashe, lamarin da ya ba ta babban taimako.

Ban da tsarin neman jinya cikin hadin gwiwa, an kuma baiwa mazauna kauyen Liang-Jia-He inshorar kulawa da tsoffi, wato tsoffi da shekarunsu suka wuce 60 da haihuwa suna iya samun kudin tallafi a kowane wata.

Mazauna kauyen Liang-Jia-He wadanda suka samun arziki yanzu sun fi dora muhimmanci kan ba da ilmi ga yaransu, har ma suna kai yaran garuruwa da gundumomi domin samun kyawawan damammakin karatu, ya zuwa yanzu dai yawan yaran kauyen da suka samu iznin shiga jami'a ya kai fiye da 10.

Yanzu Liu Jinlian ita ce mai aikin shara a kamfanin yawon shakatawa na kauyen Liang-Jia-He, tana iya samun kudin shiga yuan 1200 a kowane wata. Ita ma ta bude wani shago a gida domin sayar da shimfidar takalmi da kayayyakin musamman na wurin.

Liu Ruilian, wato wata ma'aikaciyar dinki ce a da, yanzu kuma wata mai yin aikin sa kai ne na yiwa jama'a bayani, dansa Gong Gang ya kebe kudi RMB Yuan dubu 150 ya soma tafiyar da harkokin jin dadin zama a kauye. Bugu da kari, ya bude wani kamfanin sayar da gero da dabino mai tambarin"Liangjiahe".

A shekarar 2017, yawan kudin shiga na mazauna kauyen Liang-Jia-He ya kai RMB Yuan dubu 20,826, jimillar da ta karu da kashi 15.7 cikin dari bisa na shekarar 2016.

Sakamakon bunkasuwar kamfanin yawon shakatawa na kauyen Liang-Jia-He, da kamfanin kiwon dabbobin gida, da kamfanin samar da tuffa, da kamfanin sayar da kananan kayayyaki, da ma dakunan jin dadin zama a kauye, kauyen Liang-Jia-He ya kama wata sabuwar hanyar ci gaba.

A ranar 18 ga watan Oktoba na shekarar 2017, mazauna kauyen Liang-Jia-He sun taru don sa ran ganin bude babban taro karo na 19 na wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

Rahoton da Babban sakataren JKS Xi Jinping ya gabatar ya gamsar da mazauna kauyen sosai. Cikin tattaunawarsu, sun nuna imani sosai ga kyakkyawar makomarsu.

Liang-Jia-He, wani karamin kauye ne dake yankin dutse, inda aka taba tsara burika, yanzu burikan sun zama gaske. (Kande Gao, Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China