Kwamandan rundunar ECOMIG, Colonel Fulgence Ndour, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis cewa, Abubakar Abdullahi soja ne mai mukamin Staff Sergeant a rundunar sojin Nijeriya.
Sanarwar ta ce Marigayin mai shekaru 46, ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Laraba. Ta ce an lura da yadda numfashinsa ya samu matsala ne yayin da yake barci, inda aka garzaya da shi asibiti, sai da bai rayu ba.
Rundunar ECOMIG, ta mika ta'aziyyarta ga iyalan marigayin da kuma rundunar sojin Nijeriya bisa wannan rashi.
Rundunar ECOMIG ta isa Gambia ne a watan Disamban 2016, domin tabbatar da muradin al'ummar kasar, bayan tsohon Shugabansu Yahaya Jammeh ya ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar. Rundunar ta kunshi 'yan asalin kasashen kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika, ciki har da Senegal da Nijeriya da kuma Ghana. (Fa'iza Mustapha)