in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane uku ne da son tayar da yakin cinikayya
2018-07-05 21:28:43 cri
Gobe Jumma'a 6 ga wata, kudurin da kasar Amurka ta tsaida na kara haraji kan kayan da Sin ta fitar zuwa Amurka da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 34 zai soma aiki. Yanzu kasar Sin ta shirya don daukar karin matakan da suka dace don mayar da martani. Lallai da sauki za tayar da yakin ciniki a tsakanin kasashen biyu.

Tun da aka ce yaki, to ba shakka bangarorin biyu dake yaki ba za su yi nasara ba. Don haka, kasar Sin ba ta son yin yakin cinikayya, kuma ba za ta tayar da yakin ba. Saboda ta gane, babu wanda zai yi nasara a yakin cinikayya. Idan aka tayar da yaki a tsakanin Sin da Amurka, wadanda lamarin zai shafa su ne kasashen biyu, har ma da jama'ar duniya baki daya. Amma, a kasar Amurka akwai mutane uku ba sa ganin haka.

A yanzu haka, shugaban kasar Amurka Donald Trump, da wakilin kasar dake kula da harkokin cinikayya Robert Lighthizer, da kuma daraktan harkokin cinikayyar kasar Peter Navarro suna hada kai sosai wajen amfani da hanyar kara karbar haraji don tayar da yaki da abokan cinikayyarta, inda kuma hankalinsu ya karkata ga kasar Sin

Wannan ba abun mamaki ba ne. Trump na ganin cewa, shi dan kasuwa ne, don haka ya yi amfani da wannan domin neman kuri'u a yayin da yake yakin neman zaben shugabancin kasar, inda ya mai da hankali kan kasar Sin, a cewarsa, kasar Sin ce ta kwace guraban aikin yi daga hannun Amurkawa, don haka zai taimakawa Amurkawa don dawo da guraban aikinsu. Bayan da ya zama shugaban kasa, dukkan manufofin da ya kaddamar na nufin cika alkawarin da ya yi ne a yayin da yake neman zama shugaban kasar, matakin da yake ganin zai daga matsayin jam'iyyar sa a zaben tsakiyan wa'adi da za a yi a watan Nuwamba, ta yadda zai iya kokarin ganin ya ci gaba da rike mulki. Don haka, duk manufofin cikin gida da na ketare da aka dauka a da dole su dace da umurninsa, amma ba shi ya martaba manufofin ba. Bisa wannan dalili ne, kasar Sin ta kasance muhimmin yankin yaki nasa wajen cika alkawarinsa.

Muddin yana fatan cimma burinsa, dole ne Trump ya nemi abokan hadin kai masu ra'ayin iri daya. Wannan ya sa Robert Lighthizer da Peter Navarro suka shiga ransa.

Robert Lighthizer shi ne mai tsara bincike na lambar 301, wanda ya taba halartar tarukan shawarwarin kasa da kasa kan hajojin karafa, motoci da amfanin gona sama da 20, kuma ya fara yin suna a shekarar 1985, bayan ya tilasta wa kasar Japan sa hannu kan "yarjejeniyar Plaza". Haka zalika, a shekarar 1999, ya sanar da cewa, shigowar kasar Sin cikin kungiyar WTO babban kalubale ne ga kasar Amurka, inda ya kuma zargin gwamnatin kasar Amurka cewar, bai kamata ta daina matsa wa kasar Sin lamba kan batun ciniki ba. Shi ya sa, bayan barkewar yakin ciniki a tsakanin Sin da Amurka, Robert Lighthizer ya ci gaba da kasance a sahun gaba a wannan fanni, domin yana son matsa wa kasar Sin lamba, har sai ta canja hanyarta ta neman bunkasuwa.

A nasa bangare kuma, Peter Navarro bai taba kawo ziyara kasar Sin ba har zuwa shekarar 2018, ko da yake, babban aikinsa shi ne yin nazari kan wutar lantarki da makamashi, amma, a shekarun baya bayan nan, ya yi ta nazarin "kalubalen da Sin ta samar wa kasashen duniya", har ya sha zargin kasar Sin a hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI, kwamitin binciken tsaron tattalin arziki da sauran hukumomin kasar Amurka, lamarin da ya janyo hankalin Donald Trump, har ya nada Peter Navarro a matsayin mai ba shi shawara.

Ya zuwa yanzu, Amurkawa guda uku wadanda ke son yin yakin cinikayya da kasar Sin ra'ayinsu ya zo daya, dalilin kuwa a bayyane yake, wato Donald Trump na ganin, babu wasu abubuwa sai kuri'u da takara. Kana ra'ayinsa ya yi kama da na Robert Lighthizer da kuma Peter Navarro, don haka za su dace da juna, su hada kai tare. Shi ya sa ana iya ganin cewa, a yakin cinikayyar da Amurka ke yi da kasar Sin, ayyukan da wadannan mutane uku ke yi ba daya ba ne, wato, Trump ya zama babban mai bada umurni, wanda kan yi amfani da shafin sada zumunta na Twitter don bayar da umurni; Robert Lighthizer ya zama tamkar mai takala, wanda ya kan bayar da rahotanni da kalaman shaidu game da kafa shingen cinikayya da kasar Sin ta yi. Yayin da Peter Navarro ya zama mai bada shawara, wanda ya rubuta wani littafi mai suna "Death by China", abun da ya zama mafarin yakin cinikayya da Amurka ta kaddamar kan kasar Sin ta fuskar manufofi.

Kafofin watsa labarai gami da kwararru na ganin cewa, Peter Navarro bai fahimci ainihin dalilin da ya sa aka samu rarar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ba, bai fahimta ba sam. Alal misali, mujallar The New Yorker ta ce, ra'ayin Navarro ba ma kawai na da sauki ba ne, har ma babban kuskure ne kana mai hadari. Ita kuma cibiyar Cato ta Amurka ta bayyana cewa, a cikin bayanan da Navarro ya rubuta, kusan kowace shadara na kunshe da kurakuran da suka sabawa hakikanin halin da ake ciki, ko kuma rashin fahimta. (Bilkisu, Murtala, Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China