in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin Amurka: Akwai yiwuwar Amurka ta zama 'babbar kasa marar mutunci'
2018-07-05 20:24:12 cri
Wani babban manazarci daga cibiyar Brookings ta kasar Amurka, wanda ake masa lakabin "masanin manufofin diflomasiyya a fannin ra'ayin rikau", Robert Kagan ya rubuta wani bayanin kwanan baya, inda ya yi kashedin cewa, akwai yiwuwar Amurka ta zama "babbar kasa marar mutunci".

Tun da Donald Trump ya zama shugaban Amurka, kasarsa ta janye daga wasu muhimman yarjeniyoyin kasa da kasa da dama, ciki har da yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen da suka ratsa yankin tekun Pasifik, da yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD da aka cimma a Paris, da yarjejeniyar nukiliyara Iran daga dukkan fannoni. Har wa yau, Amurka ta janye daga wasu kungiyoyin duniya, ciki har da kungiyar kula da harkokin ilimi , kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO, da kwamitin kula da kare hakkin dan Adam na MDD. Bugu da kari, gwamnatin Trump ta yi biris da kiraye-kiraye gami da gargadin da kasashen duniya suka yi mata, game da kaddamar da yakin cinikayya.

Tun lokacin da Amurka ta canja daga "babbar kasa" zuwa "babbar kasa marar mutunci", take kawo babbar barazana ga duniya baki daya, al'amarin da ya kasance wata babbar matsala ga kokarin da kasashe daban-daban ke yi na neman mafita.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China