in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin tsakiya na Afrika ta kudu ya samar da takardun kudi don tunawa da marigayi Mandela
2018-07-05 10:13:23 cri

Babban bankin kasar Afrika ta kudu (SARB) ya sanar a jiya Laraba cewa, ya fitar da sabbin takardun kudade domin tunawa da marigayi tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.

Bankin ya ce, tuni aka fara shirin wayar da kan al'umma a dukkan kafafen yada labarun kasar domin gabatar da sabbin kudaden don tunawa da marigayin kuma tuni an fidda tsabar kudade na kudin kasar Rand 5 dauke da hoton marigayin wanda tuni ya fara yawo a tsakanin al'umma don karrama marigayi Mandela.

Takardun kudaden da rand 5 masu dauke da hoton marigayin za'a fara hada hadar ciniki da su ne daga ranar 13 ga wannan wata na Yuli.

A ranar 18 ga watan Yuli ne ake cika shekaru 100 da haihuwar Mandela, a wannan lokacin za'a gudanar da gagarumin biki a duk fadin kasar ta Afrika ta kudu har ma da sauran sassan duniya. MDD ta kebe ranar 18 ga watan Yuli a matsayin ranar tunawa da Nelson Mandela ta kasa da kasa, wacce ake tunawa da irin darasin da marigayin ya bari a lokacin rayuwarsa, domin duniya ta yi koyi da shi don kyautata rayuwar bil adama a fadin duniya.

Gwamnan babban bankin na SARB Lesetja Kganyago ya ce, wannan shi ne karon farko da babban bankin kasar ya fitar da nau'in takardun kudade domin tunawa da marigayin, kuma babu wani abu mafi dacewa a lokacin tunawa da cika shekaru 100 da haihuwar Mandela da wuce daukar wannan mataki, in ji shi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China