in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rushe gwamnatin Côte d'Ivoire
2018-07-05 10:02:13 cri

Fadar shugaban kasa a kasar Cote d'Ivoire, ta bayyana rushe gwamnatin da firaminista Amadou Gon Coulibaly ke jagoranta. Wata sanarwa da babban sakataren fadar gwamnatin Patrick Achi ya fitar, ta ce da wannan sanarwa, wa'adin aikin firaminista Coulibaly ya zo karshe.

Sai dai kuma sanarwar ta sanar da sake nada Mr. Coulibaly a matsayin firaministan sabuwar gwamnatin da za a kafa, shi ne kuma zai jagoranci aiwatar da wannan aiki.

A daya hannun kuma, sanarwar ta ce dukkanin ministocin tsohuwar gwamnatin, za su ci gaba da gudanar da ayyukan ma'aikatunsu, har ya zuwa lokacin da za a rantsar da mambobin sabuwar majalissar zartawar kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China