in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira ga jagororin Sudan ta kudu da su rungumi zaman lafiya domin kawo karshen yaki
2018-07-05 09:58:27 cri

Mataimakiyar babban magatakardar MDD dake ziyara a Sudan ta kudu Amina Mohammed, ta yi kira ga jagororin Sudan ta kudu, da su rungumi hanyoyin zaman lafiya, domin kawo karshen yake yake dake addabar al'ummun kasar su.

Da take zantawa da 'yan jaridu a ranar Laraba a birnin Juba, bayan kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Sudan ta kudun, Amina Mohammed ta yi maraba da kudurin dakatar da bude wuta da sassan kasar, wadanda ba sa ga maciji da juna suka cimma, tana mai cewa, shawarwari ne kadai hanya daya tilo, da za ta kai ga warware kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu haka.

A makon da ya gabata ne dai shugaban Sudan ta kudun Salva Kiir, da tsohon mataimakinsa, kuma jagoran 'yan adawar kasar Riek Machar, suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar sulhu a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar Sudan, domin kawo karshen tashe tashen hankula da kasarsu ta shafe shekaru sama da hudu tana fuskanta.

To sai dai kuma jim kadan da hakan, sai sassan biyu suka ci gaba da kaiwa juna hare hare, suna masu dorawa juna alhakin karya alfarmar yarjejeniyar da aka cimma ba da jimawa ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China