in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin albarkatun mai na Libya ya yi kira da a ba da damar ci gaba da cinikayyar danyen mai
2018-07-05 09:26:53 cri

Kamfanin sarrafa albarkatun man fetir na kasar Libya, ya yi kira ga MDD, da ta baiwa gwamnatin rikon kwaryar kasar mai helkwata a gabashi, izinin ci gaba da hakar danyen mai.

Wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ta bayyana wannan bukata, bayan da gwamnatin ta gabashin Libya ta amshe iko da sassan rijiyoyin hakar mai daga dakarun 'yan tawaye dake yankin, suka kuma mika ikon su ga sojojin yankin.

Sanarwar ta jaddada burin kasar Libya, na biyayya ga dukkanin dokokin kamfanoni da kasashen da ke hada hadar cinikayya albarkatun mai da kasar.

A baya bayan nan ne dai jagoran sojojin gwamnatin gabashin Libya Janar Khalifa Haftar, ya bayyana cewa, bangarensu ya amshe iko da rijiyoyin mai dake yankin da suke iko da shi, wadanda ke da nisan kusan kilomita 500 daga gabashin birnin Tripoli, kuma suke kunshe da tashar danyen mai mafi girma a kasar, bayan da suka fatattaki mayakan sa kai da suka yi kaka gida a yankin. Jim kadan bayan aukuwar hakan ne kuma, sojojin suka damka wannan yanki hannun sojojin dake biyayya ga tsagin gwamnatin gabashin kasar, maimakon gwamnatin dake da helkwata a Tripoli, wadda MDD ke marawa baya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China