in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Irin Illolin Da Matakan Kare Muradun Amurka Za Su Yi Wa Tattalin Arzikin Duniya
2018-07-06 11:10:46 cri

Kasar Amurka mai yawan jihohi Hamsin (50) da al'umma sama da miliyan dari uku da ashirin da biyar (325), ta bullo da wasu matakai a karkashin shugabanta na yanzu, Mista Donald Trump da sunan kare muradunta na tattalin arziki kamar yadda shugaban ya sha nanatawa a lokacin da yake neman yakin zaben da ya kai shi hawa karagar mulki.

Trump ya lashi takobin yakar kayan da ake shigo da su daga waje zuwa cikin Amurka domin a cewarsa, ana yiwa Amurkawa sakiyar-da-ba-ruwa, sakamakon yadda ake shigo musu da kaya daga waje su cika kasuwanninsu maimakon samarwa a cikin gida.

Hujjar da shugaban yake bayarwa na daukan matakin ita ce kiyaye abubuwan da suka shafi tsaron kasa inda hakan a gefe daya kuma ya tayar da kura a tsakanin Amurka da manyan abokanta na huldar kasuwanci.

Galibin wadanda ke bibiyar abubuwan da ke faruwa, tun daga lokacin da Trump ya ayyana daukar matakin kara haraji kan kayan da ake shiga da su Amurka daga waje, sun ce kamata ya yi kafin daukar matakin, Fadar White House ta tuna da yarjejeniyar sakin marar kasuwancin da ta kulla da wasu kasashe wanda ya ba ta damar samun bunkasar tattalin arziki.

A shekarun alif da dari tara da casa'in (1990s), Amurka ta samu gagarumin cigaban tattalin arziki. Da farko a shekarar 1994, ta shiga cikin yarjejeniyar kasuwanci cikin 'yanci ta yankin kasashen Arewacin Amurka (NAFTA), wadda ta baiwa Amurkawa miliyan dari hudu da hamsin (450) damar sarrafa kayan kasuwanci da samun aikace-aikace da kudinsu ya kai Dala triliyan goma sha bakwai (17). Makasudin tsara wannan yarjejeniyar ta ranar 1 ga Janairun 2008 shi ne kawar da shingayen da suke kange huldar kasuwanci a tsakanin Amurka, Kanada da Mexico. Ko makaho ya san Amurka ta ci gajiyar wannan.

Amurka mai amfani da tsarin jari-hujja a fannin tattalin arzikinta ita ce kasar da ta fi ko wace kasa sayo kaya daga waje inda a shekarar 2010 aka bayyana cewa, ta samu gibin Dala biliyan dari shida da talatin da biyar ($635b).

Kasancewar kasar mai kunshe da mutanen da suka mallaki fiye da kashi arba'in da daya na yawan arzikin duniya kana da kusan rabin adadin wadanda suka mallaki miliyoyin kudi na duniya, wajibi ne matakin da Trump ya dauka ya yi tasiri a kan tattalin arzikin duniya.

A halin yanzu, da yake duniya ta yi ado da zamanin da ake samun zurfin binciken kimiyya da fasaha da kere-kere kuma kasar ta zama jagora a fannin kirkira a wadannan fannonin tun daga tsakiyar karni na ashirin, babu makawa kasashen da suke neman kayan fasaha don inganta hada-hadarsu a cikin gida da waje su samu koma-baya. Domin kayan da suke kaiwa kasar su sayar daga nan su sayo abin da suke so; an saka su a cikin kangin haraji.

Masana tattalin arzikin duniya daban-daban suna ci gaba da bayani kan yadda matakin na Amurka zai iya kassara tattalin arzikin duniya baki daya.

Sakataren baitul malin Birtaniya, Philip Hammond, ya bayyana a wata hira da Gidan Talabijin na CNN ya yi da shi lokacin da ya kai wata ziyara a Kasar Indiya kwanan baya cewa yakin kasuwancin zai haifar da bala'in da ba kasashen da aka yi wa abin ne kawai zai shafa ba, har da Amurkan za ta dandana kudarta, domin ta jawo ruwan dafa kanta.

Hammond ya ce bai kamata Trump ya wargaza abin da aka kulla shekaru da yawa da suka gabata ba; wanda ya ce Fadar White House ita ce ta-yi-uwa-ta-yi-makarbiya wajen tabbatar da bude kofar kasuwanci ga abokan hulda. "Sai yanzu Amurka za ta ce tana da shakku a kan sahihancin tsare-tsaren da muka yi," in ji shi.

A gargadi na karshen da ya yi wa Trump, Hammond ya bayyana fatan ganin shugaban Amurkan ya dakatar da matakin domin kauce wa shiga yakin kasuwancin gadan-gadan.

Daga lokacin da Trump ya matsa kaimi a kan matakin, kasuwannin hannayen jari a sassan kasashen da abin ya fi shafa sun fara samun nakasu. Sannan wasu kamfanoni kamar na Herley-Davidson sun fara shirin dauke masana'antar kere-keren baburansu zuwa yankin Turai daga Amurka domin kauce wa abin da ramakon gayyar da za a yi wa Amurka zai haifar.

Ko a makon da ya gabata, Birnin Brussels ya kara yawan haraji a kan kayan da ake sarrafawa daga Amurka ciki har da manyan babura, barasa da sauran su domin mayar da martani kan matakin na Trump.

Matakin da Gwamnatin Trump ta dauka na kare muradunta ba tare da la'akari da muradun abokan huldarta ba, zai cigaba da janyo martani kala-kala wanda a sakamakon hakan galibin masana tattalin arziki sun yi amannar cewa abin zai haifar da matsala ga tattalin arzikin duniya baki daya.

Shugaban sashen tuntuba kan tattalin arziki na Jami'ar Odford, Greg Daco ya bayyana cewa matakin na Trump zai janyo asarar ayyukan yi a bangaren karafa da sanholo kawai kimanin dubu saba'in (70,000), sannan karfin tattalin arzikin hada-hadar cikin gida na Amurka da Kasar Sin wadanda suke kan gaba wajen cigaban tattalin arziki a duniya zai ragu da kasa da kashi daya a cikin dari.

Kungiyoyin manyan 'yan kasuwa na Amurka da suka kunshi manyan dillalan motoci da kayan aikin gona da masana'antu, sun yi gargadin cewa matakin na Trump ba kasashen da ya kara wa harajin kaya ba ne zai shafa, su kansu abin zai tagayyara su.

A cikin wasikar da kungiyoyin 'yan kasuwan hamsin (50) suka rattaba hannu suka aike wa majalisar dattawan kasar, sun nemi 'yan majalisar su kafa dokar da za ta nemi amincewar majalisa kafin shugaban kasa ya kara yawan haraji a kan ko wane kaya daga yanzu.

A wasikar, kamar yadda kafar yada labarai ta USA Today ta ruwaito, 'yan kasuwan sun bayyana cewa, "yana kara fitowa baro-baro cewa yanayin yadda aka yi karin harajin a kan karafuna da sanholo zai haifar da ramakon gayya daga manyan abokan kasuwancinmu, inda hakan zai dankwafar da tattalin arzikin Amurka".

Kungiyoyin, wadanda ke wakiltar manyan kamfanoni ciki har da Amazon, da General Motors, da Walmart, sun ce suna matukar takaicin yadda sashe na dari biyu da talatin da biyu na dokar Amurka kan fadada kasuwanci ta 1966; ta kyale shugaban kasan ya ci karensa ba babbaka wajen kara yawan harajin kaya.

Sun jaddada goyon bayansu ga kudirin dokar da Sanata Bob Coker, dan jam'iyyar Republican ya gabatar domin sanya wa shugaban kasan linzami wajen amfani da sashen dokar 232

Har ila yau, daga cikin masana tattalin arziki 45 da Kungiyar Masana Tattalin Arziki ta NABE da ke Amurka ta yi safiyo a kansu, kashi saba'in da shida a cikin dari (76) sun ce matakin na Trump ba zai haifar wa Amurka da mai ido ba.

Galibin masana tattalin arziki a fadin duniya sun ce yakin kasuwanci tun fil'azal ba shi da riba illa tafka asara.

Kamar yadda kafar yada Labaru ta Financial Times ta ruwaito, Masanan sun ce akwai yiwuwar nan da 'yan wasu shekaru karfin tattalin arzikin duniya baki daya ya fadi da kashi daya zuwa uku a cikin dari sanadiyyar matakin na Amurka.

Suka ce a duk lokacin da aka kara wa kaya haraji, abin zai shafi kasuwanci a tsakanin kasashen duniya, daga nan sai a samu raguwar hada-hadar kayan da ake fitarwa zuwa waje da wadanda ake shigo da su cikin kasa. Wannan ne yake sanya hada-hadar ta yi dogon sumar da sai an yi da gaske kafin ta farfado.

Wata matsala da karin harajin zai haifar ita ce hana bunkasar tattalin arzikin duniyar cikin hanzari saboda abin da ake nema na cigaban kasuwanci a tsakanin kasashen duniya ba zai samu ba. A yanzu haka, an kiyasta cewa hada-hadar tattalin arzikin duniya ta kai kimanin Dala tiriliyan saba'in da biyar da bilyan dari uku ($75.3t). Kuma manyan kasashen da suke da mafi karfin tattalin arziki a duniyar su biyu da ke hararar juna a yanzu saboda batun kara harajin, Amurka da Kasar Sin, su ne ke da mallakar kusan rabin wannan adadin.

Matakin na Amurka zai iya zama kaikayi-koma-kan-mashekiya, kasancewar akwai manyan kamfanonin kasar da suke baje kolin kayansu a Kasar Sin domin cin gajiyar rahusan aikin da ake samu a kasar.

Haka nan sauran kayan da abin zai shafa sun hada da kayan asibiti, magunguna da waken soya da ake shigar da su cikin Sin daga Amurka.

An ruwaito wani masanin tattalin arziki dan Kasar Indiya, Irvin Seah yana bayyana cewa akwai fargaba sosai kan yakin kasuwancin da Amurka ke neman tayarwa a duniya. Domin baya ga manyan kasashen da abin zai shafa, sauran kananan kasashen da suke dogaro da kasuwanci a tsakaninsu da kasashen duniya su ma abin ba zai yi musu kyau ba. Daga nan tattalin arzikin duniya baki daya zai girgiza.

Babu mamaki a samu maslaha kan batun; idan Sin da sauran manyan kasashen da suke kasuwanci da Amurka suka sassauto, shi ma Trump ya gangaro don a hadu a tsakiya. Sai dai lokaci ne kadai zai iya tabbatar da hakan domin duka bangarorin biyu sun nuna a shirye suke komai-ta-fanjama-fanjam!

(Abdulrazaq Yahuza Jere, Editan LEADERSHIP A YAU JUMA'A, daga Nijeriya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China