in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawa a tsakanin masanan kasar Sin da na kasashen Afirka
2018-07-04 15:50:55 cri

A yau ne aka bude taron dandalin tattaunawa tsakanin kwararrun masana na kasar Sin da kasashen Afirka karo na bakwai a nan birnin Beijing. Jakadun kasashen Afirka 44 da ke nan kasar Sin da jami'an gwamnati da shehunan malamai da kuma wakilan kafofin yada labarai daga kasashen Afirka 52, da kuma jami'an da suka fito daga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar da masanan kasar baki daya sama da 380 ne suka halarci taron.

A wajen bikin bude taron, Chen Xiaodong, mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Sin ya gabatar da Jawabi, a jawabin nasa ya ce, bana shekaru 40 kenan da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kuma a watan Satumba mai zuwa ne za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Shekarun 40 da suka shude sun kasance shekaru na ci gaban Sin da Kasashen duniya tare, haka kuma shekaru 40 ne da Sin da kasashen Afirka ke neman cigaba kafada da kafada. Ya jaddada cewa, kasar Sin na tsayawa ga aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ba tare da gindaya sharudan siyasa ba, kana tana tsayawa ga sa kaimin ci gaban tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma na kasashen. Sa'an nan tana tsayawa ga samun moriyar juna.

Taron ya kasance daya daga cikin tarukan share fagen taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da za a gudanar a watan Satumba dake tafe. A wajen bikin na yini biyu, mahalarta taron zasu tattauna bisa babban jigon nan na "huldar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka a yayin da Sin ke yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China