in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunisiya da Sin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar raya tattalin arziki na zamani
2018-07-04 10:43:10 cri

Kasashen Tunisiya da Sin sun sanya hannu kan yarjejeniyar raya tattalin arzikinsu ta hanyar fasahohin zamani, cibiyar nazarin dabarun tsare tsare ta Tunisiya (ITES) ce ta tabbata da hakan.

An cimma yarjejeniyar ne a lokacin taron karawa juna sani da aka gudanar kan raya tattalin arziki ta hanyar fasahohin zamani karkashin shawarar ziri daya da hanya daya wanda aka gudanar a birnin Beijing.

ITES ta ce, wannan yarjejeniyar za ta samarwa matasan Tunisiya damammaki, musamman wadanda suka karanci fannonin sadarwa, da fasahohin hada layukan na'ura mai kwakwalwa, da cinikayya ta hanyar yanar gizo da makamantansu.

Neji Jalloul, shi ne babban daraktan cibiyar ta ITES, ya bayyana cewa, dangantakar cinikayya tsakanin kasashen Tunisiya da Sin tana kara bunkasuwa sannu a hankali kuma cikin kyakkyawan yanayi.

Jalloul ya ce, sabon tsarin ciniki ta hanyar siliki ya hade kasashe masu yawa daga nahiyoyin Asiya, Turai da Afrika, kana ya baiwa kowa damar yin hadin gwiwa da juna, da raya tattalin arziki, da musayar al'adu da kuma yin cudanya ta hanyar na'urorin zamani.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China