in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kauyen Liang-Jia-He(4)
2018-07-04 09:03:34 cri

A watan Janairun shekarar 1974, lokacin dari ne sosai a yankin tsaunin da ake kira Huangtu Gaoyuan, kuma ba da jimawa ba za a fara bikin bazara, mazauna kauyen kuma suna kokarin shirya bikin.

Xi Jinping, wanda ba da dadewa ba aka zabe shi sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke kauyen yana tunanin abin da zai iya yi domin yin gyaran fuska ga kauyen.

A wannan rana, yayin da Xi Jinping ya ke karanta jarida, inda wasu rahotanni biyu da jaridar People's Daily ta wallafa a ranar 8 ga wata ya jawo hankalinsa, rahotannin da suka shafi yadda ake kokarin samar da iskar gas daga najasa. Me zai hana mu ma mu yi amfani da nau'in iskar gas a wurinmu wajen dafa abinci da kuma samar da wuta?

Amma kauyen Liang-Jia-He yana wajen karkara, sai an yi tafiyar kilomita 100 idan ana bukatar kwal. Lalle an jima ana sare bishiyoyi domin samar da wutar da ake bukata wajen dafa abinci, abin kuma da ya kan haifar da zaizayewar kasa. Amma idan an yi kokarin samar da iskar gas daga najasa, ba kawai zai kai ga warware matsalar makamashin da ake bukata a kauyen ba, har ma ta hanyar sarrafa najasa za a kyautata kiwon lafiya a kauyen tare kuma da samar da takin da ake bukata a ayyukan gona. Ai nau'in iskar gas ta kasance bakin zaren warware matsalolin da ake fuskanta a kauyuka.

Duk da cewa buri ne mai kyau, amma Xi Jinping sai da ya natsu ya yi tunani, yanayi ya bambanta sosai a lardin Sichuan da arewacin lardin Shaanxi, da gaske za a iya bunkasa wannan hanya?

Kullum Xi Jinping ya kan dauki matakai a maimakon yin tunani, don haka ya yanke shawarar zuwa lardin Sichuan domin gano amsar wannan tambayar.

Ya yi tafiyar kilomita sama da 20 da kafa zuwa wajen garin, inda ya bayyana shawararsa ta bunkasa ayyukan samar da iskar gas daga najasa ga mahukuntan garin, shawarar da ta samu amincewa. Don haka, bayan bikin bazara, Xi Jinping ya tara kudaden da suka bukata, ya kama hanyar zuwa lardin Sichuan tare da wasu jami'ai uku.

Malam Yang Chao, wanda a wancan lokaci shi ne mataimakin shugaban sashen yayata harkokin samar da iskar gas daga najasa, ya shafe tsawon shakaru takwas yana aiki a yankin Yan'an kafin kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Ya karbe su da hannu bibbiyu, inda ya yi musu bayani a kan yadda ake samar da iskar gas daga najasa a lardin na Xichuan, ya kuma ba su damar zuwa sassan nazarin samar da iskar gas daga najasa don su ganewa idonsu

Ziyarar ta karfafa gwiwar Xi Jinping ta bunkasa ayyukan samar da iskar gas daga najasa a kauyen Liang-Jia-He, sai dai matsaloli masu yawa sun wuce tunaninsa.

Matsala ta farko ita ce a ina za a haka ramin sarrafa najasa domin samar da nau'in gas, kasar da ke farfajiyar gidajen mazauna kauyen tana da laushi sosai, wadda ba ta dace da haka irin wannan ramin ba. Sa'an nan, hanyoyin zuwa kauyen kanana ne wadanda ba su dace da shigowar motocin sufurin suminti da duwatsu da ake bukata. Har wa yau, mazauna kauyen suna zama ne a barbaje, in har an kai ga gina ramin, yaya za a samar da iskar da aka samu zuwa ko wane gida? Babbar matsalar kuma ita ce, ana bukatar dutse na musamman wajen rufa ramin sarrafa najasa, amma ba a samun nau'in dutsen a kauyen.

Matsala tana daukar matakai. Babu dutsen da ake bukata, Xi Jinping ya jagoranci mazauna kauyen su haka kasa har sun kai ga fitar da dutwasu daga zurfin kasa da ya kai mita daya. Babu rairayi kuma, sai Xi Jinping ya jagoranci wasu matasa su je wani wurin da ake kira Qianmagou da ke da nisan kilomita takwas, su dauko rairayi a cikin jakkuna. Haka kuma babu farar kasa, don haka ya je wurin malamai ya koyi yadda za a sarrafa ta, har ma ya kafa wata karamar masana'antar samar da farar kasa, don samar da farar kasa da ake bukata.

Sabo da niyyarsa, Xi Jinping ya yi ta fama da aikin, sai dai akwai sabanin ra'ayin da aka bayyana. A gaban Xi Jinping da ke kokarin haka rami, wasu sun ce, "Ka daina, akwai dumi a lardin Sichuan, amma akwai sanyi a Yanchuan, aikin bai dace da wajenmu ba, nau'in iskar gas ba za ta yi a yankinmu ba."

Amma Xi Jinping ya kare aniyarsa, kuma a sakamakon niyyarsa da kuma kokarinsa, a tsakiyar watan Yulin shekarar 1974, an cimma gina wani ramin sarrafa najasa da ke da fadin mita takwas. Amma lamarin bai sa shi farin ciki ba, dalili kuma shi ne bayan da aka hada shi da bututu, iskar gas ba ta fito ba.

Mece ce matsalar? Ko bututun ne ya toshe? Daga karshe, Xi Jinping ya gano matsala daga bututun, ya samo wata sandar karfe, ya zungura a ciki, nan da nan ruwan najasa ya fito har ya bata fuskarsa, nan da nan aka fara jin karar iska daga bututun.

Ba tare da bata lokaci ba, ko fuskarsa bai wanke ba, ya sake hada bututun, ya kyarta ashana, lalle, kwalliya ta biya kudin sabulu, sai wuta ta kama.

An samu nasara! Kowa ya ji bishara, mutane na zuwa daga sassa daban daban domin su gane ma idanunsu wannan wuta mai ban mamaki kuma mai tsabta.

Wutar da ta kama ta shaida cewa, ana iya samar da iskar gas daga najasa a yankin. Da al'umma su ka ga yadda iskar ke saukaka rayuwarsu, sai su ka samu kwarin gwiwa sosai.

Wannan nasara ta kuma jawo hankalin mahukuntan yankin, har ma hukumar Yanchuan ta sanya burin samar da iskar gas daga najasa a fadin yankin ya zuwa shekarar 1977, kuma a hukunce ta tura tawaga zuwa lardin Sichuan don ta koya.

"Tafiya mabudin ilimi", irin yanayi da al'adu na lardin Sichuan ma sun burge Xi Jinping sosai. A lokacin ziyarar, ya yi amfani da duk wata dama ta fahimtar yanayin rayuwar al'ummar wurin. He Yingui, wanda ya je tare da shi ya ce, Xi Jinping mutum ne mai sha'awar karatu da tunani, wanda kuma ya kan jaddada hada ilmi da daukar matakai a lokaci guda.

Yayin da ya koma Yanchuan, bayan da mahukuntan garin suka saurari rahotonsu game da ziyarar, nan da nan suka tsai da kudurin raya ayyukan samar da iskar gas daga najasa a fadin yankin. Daga nan aka fara shirya kwasa-kwasai, kuma Xi Jinping ne ya kan ba da lacca da bayanai game da wannan aiki.

Sai dai sabbin matsaloli sun bullo a yayin da ake haka ramin sarrafa najasa. Domin daidaita matsalar karancin duwatsu a kauyen Liang-Jia-He, an yi amfani da kasa a maimakon duwatsu, inda aka kirkiro ramin da aka gina da kasa da kuma duwatsu, an kuma yi amfani da kasa da aka dandabe ta sosai a maimakon sumunti. Ta hakan, kudin haka ramin ya kuma ragu daga yuan 40 zuwa 30. Ya zuwa watan Agustan shekarar 1975, an gina ramuka irin wannan 34, wadanda suka warware matsalar makamashin da ake bukata wajen fitila da dafa abinci ga iyalai 43 a yankin.

Wannan aiki na gina ramukan sarrafa najasa domin samar da iskar gas ya yi babban tasiri ga Xi Jinping.

Bayan shekaru 15, Xi Jinping wanda a lokacin shi ne sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke yankin Ningde na lardin Fujian ya tuna da cewa, "Lokacin da nake kauyen Liang-Jia-He, mun gina ramukan sarrafa najasa domin samar da iskar gas, inda muka amfana daga wannan aiki na bunkasa fasahohin kimiyya. Domin wannan iskar gas, ba sai an kona itace a lokacin dafa abinci ba, haka kuma ba sai an yi amfani da mai wajen kunna fitila ba, har yanzu na kan tuna da irin walwala da murna da ke fuskokin al'umma. Abin ya shaida mana cewa, da ci gaban fasahohin kimiyya ne za a warware matsalolin rayuwa, kuma za a samu goyon bayan al'umma."

A halin yanzu, an samar da wutar lantarki a kauyen Liang-Jia-He, sai dai an adana rami na farko da aka gina a karkashin jagorancin Xi Jinping, an kuma rubuta cewa wannan ne ramin sarrafa najasa domin samar da iskar gas na farko a lardin Shaanxi, domin ya zama wata alamar tarihi. Baya ga haka, hanyar da aka fadada a lokacin domin gina ramukan, har yanzu al'umma na amfani da ita.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China