in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin jam'iyyun dake kan karagar mulkin kasashen gabashin Afirka sun yabawa tunanin jam'iyyar kwaminis ta Sin
2018-07-03 14:06:23 cri

Shugabannin jam'iyyun dake kan karagar mulkin kasashen Tanzania da Kenya da Uganda da Congo Kinshasa sun bayyanawa 'yan jarida na gidan rediyon kasar Sin CRI a kwanakin baya cewa, sun yabawa manufofin jam'iyyar kwaminis ta Sin na sarrafa kasa, tare da fasahohin da aka samu, sun kuma bayyana cewa, ya kamata jam'iyyunsu su koyi tunanin jam'iyyar kwaminis ta Sin, wajen gudanar da ayyuka domin jama'a da kuma raya jam'iyyar domin kasa.

Ga cikakken bayanin da abokiyar aikinmu Zainab ta kawo mana:

Sabon babban sakataren jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi ta kasar Tanzaniya Bashiru Ally ya bayyana cewa, jam'iyyarsa da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suna da ra'ayi kamar iri daya kan raya kasa, dukkansu sun yi imani cewa, tilas ne a samu bunkasuwa bisa burin kawo moriya ga jama'a, wannan hanya daya kawai ce da ta jagori jama'a wajen kawar da talauci, duhun kai, da cututtuka tare da jin dadin rayuwarsu. Ya ce,

"A cikin shekaru 97 da aka kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an samu babban canji a kasar Sin, mutane fiye da biliyan daya sun fita daga talauci. Dalilin da ya sa Sin ta samu babbar bunkasuwa shi ne jama'ar kasar Sin sun yi imani da kansu, da neman hanyar bunkasa na tsarin gurguzu dake dacewa da zamani, da yanayin da ake ciki mai alamar kasar Sin. Don haka, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta zama jam'iyyar dake gudanar da ayyukan kasar Sin yadda ya kamata ba tare da cin hanci da rashawa."

Babban sakataren jam'iyyar Jubilee ta kasar Kenya Raphael Tuju ya yi nuni da cewa, a karkashin jagorancin tsarin tunani mai karfi, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta jagori jama'ar kasar Sin da samun nasarori da dama, ya kamata jam'iyyarsa ta koyi fasahohinta, don taimakawa kasar Kenya wajen cimma burin raya masana'antu a kasar. Ya ce,

"Da farko ya kamata mu koyi jam'iyyar kwaminis ta Sin game da yadda za a hada jama'a da membobin jam'iyyar. Ana bukatar jam'iyyarmu ta maida tsarin tunani mai karfi a matsayin tushen raya jam'iyyar. Muna bukatar yin koyi da jam'iyyar kwaminis ta Sin, ta haka za a taimakawa kasar Kenya, ta samu bunkasuwa cikin sauri a gajeren lokaci."

Mataimakin babban sakataren jam'iyyar National Resistance Movement Organization ta kasar Uganda Richard Todwong ya bayyana cewa, a cikin shekaru 40 da aka bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a kasar Sin, musamman bayan babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta shaida wa kowa karfin bada jagoranci da gudanar da ayyuka, jam'iyyarsa ta yabawa tunanin gudanar da ayyuka na jam'iyyar kwaminis ta Sin, tana fatan za a kara yin hadin gwiwa da mu'amala tare da jam'iyyar kwaminis ta Sin a fannonin yaki da talauci da samun bunkasuwa mai dorewa. Ya ce,

"Yaki da talauci yana shafar jama'ar kasar, kasar Sin ta maida hankali sosai kan wannan fanni. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi la'akari da jama'a, da yaki da talauci, da warware matsaloli, don sa kaimi ga samun bunkasuwa a kasar. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana da karfin sa kaimi ga jama'a, ta yadda za su gudanar da ayyuka yadda ya kamata, kana tana maida hankali sosai ga jama'a."

Mataimakin babban sakataren jam'iyyar neman sake gina kasa da demokuradiyya ta kasar Congo Kinshasa Ferdinand Kalumbi ya bayyana cewa, a matsayin jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar, jam'iyyarsa tana son koyi fasahohi daga jam'iyyar kwaminis ta Sin kan yadda za a warware matsaloli da samun babban ci gaba, da kuma yadda za a kiyaye demokuradiyya da samun goyon baya daga jama'a.

"Ana bukatar jam'iyyarmu, ta bi tunanin demokuradiyya kamar jam'iyyar kwaminis ta Sin ke yi, da sa jama'a su san manufofinmu da na gwamnatin kasa, ta haka ne za a hada kai wajen raya tattalin arziki, da kawar da talauci, da tabbatar da tsaron kasa, da samar da amfanu ga jama'a gaba daya." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China