in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kauyen Liang-Jia-He (3)
2018-07-03 10:58:27 cri

A farkon lokacin isar Xi Jinping da sauran abokansa matasa kauyen Liang-Jia-He, bisa ka'idojin da aka tsara, a kowace rana suna cin abinci a gidajen manoman kauyen. Wainar garin masara da wainar garin wake su ne abincin da ake ba su. A wancan lokaci su ne abinci masu daraja da dadin ci, manoma ba su da damar cin su. A lokacin da matasan na Beijing suke cin abinci, yaran manoma su kan tsaya a gefe. Rayuwar da matasa suke fuskanta a kauyen na da bambanci sosai idan an kwatanta ta da ta birnin Beijing, amma zaman rayuarsu ta fi ta manoman kauyen kyau. A kauyen Liang-Jia-He, yawan hatsin da kowane manomi kan samu, kilo 10 ne kawai a kowane wata, wato bai kai rabin abun da aka samar wa matasa daga birni ba. Manoma su kan sa dusan alkama da wasu ciyayin da suke samu a daji, har a kan sa da ganyen alkama a cikin wainar domin su cika cikinsu.

Daga baya, matasan suka fara dafa abinci da kansu. A nan ne wadannan yara da suka fito daga birane suka gane cewa dafa abinci ba abu ne mai sauki ba. Da farko dai, matsalar da aka samu ita ce ta rashin itacen girki. A kan duwatsu, babu itatuwa, kuma babu bishiyoyi, a ina za a iya samun itacen girki? Manoman kauyen su kan tara itacen girki, ciki har da kashin shanu na yau da kullum. A lokacin da ibtila'in ambaliyar ruwa ya faru, ko da yake akwai hadari sosai, manoma sun nufi kogi domin tattara itatuwa. Bugu da kari, manoma su kan hau kan wasu duwatsu masu gangare domin datsa wani karamin itace nau'in Sophora. Irin wannan itace na daukar lokaci kan ya kone, amma mutane da yawa sun mutu ko sun raunana saboda nemansa a kan dutse mai gangare.

Matasan da suka fito daga birane ba su iya hawan dutse mai gangare ba balle samun karamin itacen Sophora, babu sauran hanya sai dai su samu ciyayi. A idonsu, sun samu ciyayi da yawa, amma idan sun sanya su cikin murhu, mintoci kadan kawai suke dauka kan su kone kurmus. Ciyayin da matasa 6 kan samo, ba sa isa a dafa abinci sau daya. Sannan, kwamitin kauye ya yarda da su yi amfani da goran masara da aka ajiye a lokacin da suke dafa abinci, hakan ya warware matsalar rashin itacen girki da suke fuskanta.

Kullum ana jin yunwa. A wasu lokuta, kwamitin kauyen ya kebe wa wadannan matasa garin alkama domin kyautata zaman rayuwarsu. Gong Fuzheng ya ce, wata rana, Xi Jinping ya tafi wajen gonaki tare da wainar garin alkama. A lokacin da aka fara cin abincin rana, sai ya ga manoman kauye suna cin wainar da aka yi da dusan alkama, abun da ya sa shi jin kunyar cin wainarsa ta garin alkama. Nan da nan ya raba wannan waina ga mata, bayan shi da kansa bai ci abincin rana ba.

A yayin da yake da zama a kauyen Liang-Jia-He, sau daya Xi Jinping ya taba cin abincin shinkafa kwano daya. Wannan ne karo daya kadai da ya ci shinkafa a cikin shekaru 7 da ya yi a Liang-Jia-He. A wancan lokaci, babu shinkafa a yankin arewacin Shaanxi, a wasu bukukuwa mafi muhimmanci ma ba a iya samun shinkafa. Li Yintang ne ya ba shi wannan shinkafa kwano daya.

Li Yintang, wani ma'aikaci ne a birnin Tongchuan, shi kuma abokin arziki ne na Xi Jinping. Wata rana, Li Yintang ya koma gida da shinkafa, inda ya nemi mahaifiyarsa da ta dafa shi domin yana son bai wa Xi Jinping. Mamar Yintang ta wanke shinkafa ta dafa kwano daya, sannan ta nemi Yintang ya bai wa Xi Jinping nan da nan.

Xi Jinping ya ji dadin tausayin da manoman kauyen Liang-Jia-He suke nuna masa. Ya ce, "idan na ji yunwa, abokai manoman su kan dafa min abinci. Da tufafina sun yi datti, su kan taimaka sun wanke su. Har ma idan riga ta yage, su kan taimaka sun dinke ta……"

Al'ummar kauye ba ta da sarkakiyya. Ma'aunin tabbatar da da'ar mutum shi ne, idan kana shan wahala, kuma kai mutumin kirki ne, tabbas za a mutunta ka. A lokacin da Xi Jinping yake da zama a kauyen Liang-Jia-He, aikin da ya kan yi shi ne gina madatsar ruwa.

A wancan lokaci, babu manyan injuna a kauye. A lokacin da ake gina madatsar ruwa, dole ne manoma su shimfida tabon kasa daya bayan daya bisa karfinsu, sannan su yi amfani da wani babban dutse a bubbuga tabon don ya zauna sosai. Wannan aiki yana taba karfin mutum sosai.

Bugu da kari, babu hanyar kare wadanda suke yin wannan aiki, kuma babu safar hannu. Xi Jinping ya kan dauki dutsen buga tabon. Idan ya yi yini daya yana aikin, tabbas sai ya samu bororon jini da yawa a hannayensa. Amma babu hutu, a kwana na biyu, ya sake komawa wurin ya ci gaba da aikin, abun da ya haddasa bororon jinin kara tsananta. A cewar sharhin manoman kauyen, duk da ya gaji, kuma ya sha wahala sosai, "Jinping na yin kokari matuka a kullum kan aikin."

A kan yi wannan aikin gina madatsa ne a lokacin sanyi saboda babu aikin gona da yawa a wannan lokaci, aikin gina madatsa ya fi wuya ga manoma. Manomi Liang Youchang ya tuna da cewa, a wata na biyu da na uku bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kankarar yankin arewacin lardin Shaanxi ke fara narkewa, Xi Jinping ya kan tsallake cikin ruwa mai sanyi sosai domin yin aikin gona.

Sabo da haka, manoma sun gamsu da Xi Jinping wanda ya kan yi kokari sosai kan aiki, su kan yaba masa da cewa, "saurayi ne mai kwazo."

A lokacin da Xi Jinping yake kokarin zama manomi, ya yi kokari wajen neman ilimi daga littattafai.

Manoman kauyen Liang-Jia-He sun ce, Xi Jinping ya kan dauki wani littafi mai kauri kamar wani tubali. Yana karantawa a lokacin da yake cin abinci, ya kuma karanta shi a lokacin da yake kiwon awaki.

A wancan lokaci, wato yau shekaru 50 da suka wuce, babu wutar lantarki a kauyen Liang-Jia-He, bayan dare ya yi, duhu kan lullube kauyen Liang-Jia-He, manoma ma su kan shiga barci da wuri. Amma ana iya ganin haske daga gidan da Xi Jinping yake kwana. Ba wanda ya san cewa, wannan haske maras karfi zai kawo wa Xi Jinping wata kyakkyawar makoma.

Xi Jinping ya karanta dimbin littattafan marubutan kasar Rasha. Xi Jinping ya taba tunawa da cewa, "Littattafan Rasha sun yi tasiri sosai ga duriyarmu, alal misali na karanta littafin 'Yaya Za A Yi' na Nikolay Chernyshevsky a kauyen Liang-Jia-He. A cikin wannan littafi, Lakhmeitov ya yi barci a kan bargon dake da dimbin kusoshi domin gyaran halayyarsa duk da jikinsa ya ji rauni yana fitar da jinni. A wancan lokaci, a ganinmu, idan ana son gyaran halayya, dole ne mu dauki matakai kamar haka. Sabo da haka, ba mu shimfida bargo kan gado ba, mu kan yi barci ne a kan katako kawai. Idan an yi ruwan sama ko dusar kankara, mu kan yi wasa a waje. A lokacin da ake ruwan sama, muna tsayawa a waje sai ruwan sama ya ratsa jikinmu. A lokacin da ake dusar kankara, ba mu sa riga, muna amfani da dusar kankara mu tausasa jikinmu, sannan mun yi wanka da ruwan sanyi sosai. Wannan littafi ne ya kawo mana irin wannan tasiri."

A lokacin da yake da zama a kauyen Liang-Jia-He, Xi Jinping ya kan nemi littattafai a ko'ina. Akwai wata mujalla "Furen Dutse" da hukumar gundumar Yanchuan ta wallafa ta kuma zama abin da yake karantawa. A wannan mujalla, Xi Jinping ya san Lu Yao, wanda ya zama wani shahararren marubuci a nan kasar Sin a baya. Su biyu sun taba yin hira, har Lu Yao ya taba fadin cewa, ya girmi Xi Jinping da shekaru 4, amma ilimin da Xi Jinping yake da shi ya zarce nasa, kuma ya tsara buri na dogon lokaci.

Bayan isar Xi Jinping kauyen Liang-Jia-He shekaru 2 ko 3, ya koyi magana da yaren yankin Yanchuan kamar yadda mutanen wurin suke magana.

Xi Jinping ya yi kokari sosai wajen koyon aikin gona, ciki har da aikin daidaita gonaki, sufurin kashin dabbobi, sare gonaki, girbin hatsi da dai makamatansu. Idan yana da tambaya, ya kan nemi manoma da su koya masa, sannu a hankali ya san komai har ya mallaki dukkan fasahohin aikin gona gaba daya, har ma ya kware sosai.

Bugu da kari, Xi Jinping ya kware sosai kan dukkan ayyukan da manoma suke yi. Ya samu fasahar dinkin riga, da dinkin bargo da dai sauransu.

Manoman kauyen Liang-Jia-He sun koyar wa Xi Jinping dabarar zaman kauye, Xi Jinping ma ya koyar da su ilmin boko.

A kauyen Liang-Jia-He, akwai wani mutum da ya kasance kamar wani "bata gari", ya kan yi sata. A wata rana, a lokacin da yake satar albasa, aka cafke shi. Bisa al'adar da aka saba a kauyen, aka shirya wani taro, inda mambobin kauyen suka tuhume shi bi da bi. Amma Xi Jinping bai tuhume shi ba, ya gaya masa wasu hujjoji daya bayan daya, kuma yana fatan zai gyara halayyarsa da kansa. Daga karshe dai wannan "bata gari" ya amince da ra'ayoyin Xi Jinping.

Matakin daidaita batun da Xi Jinping ya dauka ya samu amincewa daga manoman kauyen Liang-Jia-He, har ma suka ce "wannan saurayi na Beijing yana da basira!" Lalle wannan mutumin, wato "bata gari" a idon sauran mutanen kauyen, ya fara gyaran halayyarsa, ya fara aikin gona a kauyen, har ma ya zama wani mamban na gari. Daga baya, a lokacin da Liang Yuming ya yi hira da Xi Jinping kan lamarin, Xi Jinping ya ce, wannan mutum "kananan laifuffuka ya yi, tabbas za a iya gyara halayyarsa. Ya kamata mu taimakawa irin wannan mutum."

Mutunta sauran mutane, sannan taimako, har ma da hada kan mutane, Liang Yuming ya yi tsammanin cewa, wannan saurayin birnin Beijing wanda ba shi da surutun banza, yana da tunani. Sabo da haka, ya kan tattauna kan wasu matsaloli da Xi Jinping domin neman dabarun warware su.

Sannu a hankali, dakin da Xi Jinping yake zaune a kauyen Liang-Jia-He ya zama wata cibiya. Mutane na son zuwan dakinsa domin yin hira da shi, da kuma sauraran labarun tarihi da sauran labaru da suka faru a sauran wurare da Xi Jinping ke ba su. A hakika dai Xi Jinping ya zama wani mamba na kauyen Liang-Jia-He. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China