in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A madadin kasashe 140, Sin ta fidda sanarwar hadin gwiwa ta kare hakkin bil Adama
2018-07-03 10:29:07 cri

Yayin taron kwamitin kare hakkin bil Adama na MDD karo na 38, da ya gudana a Jiya Litinin, zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin MDD na birnin Geneva, kana sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, jakada Yu Jianhua, ya fidda wata sanarwar hadin gwiwa mai taken "Mai da hankali kan zaman rayuwar al'ummomin kasa da kasa, ingantawa da kare hakkin bil Adama", a madadin mambobin kungiyar 'yan Ba-Ruwanmu da kuma kasar Rasha mai kimanin kasashe 140.

Cikin jawabin da ya gabatar, Mr. Yu ya yi kira da a mai da hankali kan harkokin al'umma, domin ingantawa da kuma kare hakkin bil Adama, tare da hada kai wajen raya harkokin hakkin bil Adama cikin yanayi mai kyau.

Jawabin da ya gabatar, ya nuna ra'ayin kasashe masu tasowa, wanda kuma ya samu amincewa daga bangarori daban daban. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China