in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da goyon-bayan kyautata alaka tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu
2018-07-02 20:29:52 cri
Yau Litinin, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lu Kang ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da nuna cikakken goyon-baya ga daidaita dangantaka tsakanin Koriya ta Arewa da ta Kudu, tana kuma fatan kasashen duniya za su kara ba su kwarin-gwiwa.

Rahotanni na cewa, a kwanakin nan, Koriya ta Arewa da ta Kudu na ci gaba da yin mu'amala da juna. Game da haka, Lu Kang ya ce, kasar Sin na matukar farin-cikin ganin cewa, bangarorin biyu na kara tuntubar juna da cimma matsaya daya kan karin fannoni.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China