in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Jordan ya kaddamar da gangamin taimakawa 'yan gudun hijirar Syria
2018-07-02 10:14:41 cri

Firaministan Jordan Omar Razzaz, ya kaddamar da wani gangami jiya Lahadi a fadin kasar, da nufin samar da taimako ga al'ummar Syria dake gudun hijira a cikin kasarsu.

Wani jawabi da aka wallafa a shafinsa na Twitter na cewa, gangamin na da nufin rage walhalhalun jama'ar Syria tare da kai dauki ga wadanda ke bukata.

Firaministan ya ce, suna sanar da fara gangamin samar da agaji domin taimakawa jama'ar Syria dake cikin Syrian, domin rage wahalar da suke ciki, yana mai cewa, za a mika taimakon ne ta hannu gidauniyar Hashemite ta kasar Jordan.

Har ila yau, wani jami'in gwamnatin Jordan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiyan cewa, manyan motocin dakon kaya 17 na kasar, dake shake da kayayyakin agaji, sun shiga yankunan Syria, inda aka kai su ga al'ummar kasar dake yankin kan iyakar Jordan, wadanda rikici a yankin kudancin Syria ya tilasta musu tserewa daga matsugunansu

Wata majiya ta kara da cewa, dakarun Jordan na sanya ido kan aikin rabon kayayyakin, bayan sun tuntubi bangarori masu yaki tare da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta domin kai kayayyakin agajin.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China