in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kauyen Liang-Jia-He(2)
2018-07-02 16:13:13 cri

A zuciyarsa, Xi Jinping ya dade da ganin cewa, shi dan birnin Yan'an ne.

A ranar 14 ga watan Agustan shekara ta 2004, Xi Jinping, wanda a lokacin yake a matsayin sakataren zaunannen kwamitin lardin Zhejiang na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya zanta da gidan rediyo da talabijin na Yan'an, inda ya amsa tambayar da aka yi masa ta "ko shine ya mayar da kansa a matsayin dan asalin Yan'an?" Xi ya amsa ba tare da wani jinkiri ba yana mai cewa: "Hakikanin gaskiya ina daukar kaina a matsayin dan asalin Yan'an, saboda a nan ne na dubi tarihi kana na bude sabon babi a dukkan zaman rayuwata. Ra'ayoyi gami da halaye da dama da nake da su a halin yanzu, a Yan'an ne na samu asalinsu, don haka babu shakka ni na mayar da kaina a matsayin dan asalin Yan'an."

A ranar 22 ga watan Disambar shekara ta 1968, shugaban kasar Sin na wancan lokaci, marigayi Mao Zedong ya yi kira da cewa, ya kamata matasa masu ilimi su shiga yankin karkara, su karo ilimi, su yi koyi daga manoma, abun dake da matukar bukata gare su, inda dalibai matasa miliyan 17 a duk fadin kasar suka amsa wannan kiran, suka bar biranensu suka shiga yankunan karkara, inda suka fara zaman rayuwarsu mai burgewa.

Matashi Xi Jinping shi ma ya kasance daya daga cikin wadannan dalibai, inda ya tashi daga Beijing, fadar mulkin kasar Sin, zuwa birnin Yan'an, wanda ya kasance wani muhimmin wuri na yin juyin-juya-hali a tarihin kasar Sin.

A ranar 13 ga watan Janairun shekara ta 1969, tashar jiragen kasa ta Beijing na cike da mutane makil. Jirgin kasa dake dauke da matasa dalibai ya ratsa ta lardin Henan, sa'annan ya nufi yamma, da ya isa birnin Xi'an, jirgin ya nufi arewa, a karshe dai ya isa Tongchuan. Bayan da suka karya kumallo a Tongchuan, wadannan dalibai sun shiga cikin manyan motoci, wadanda suka je birnin Yan'an.

A ranar 16 ga watan Janairun, Xi Jinping gami da sauran wasu dalibai sun isa kungiyar jama'a ta Wen An Yi dake gundumar Yanchuan. Daga bisani kuma, sun bazu zuwa rukunonin gudanar da ayyuka daban-daban dake wurin.

An tura Xi Jinping da sauran wasu dalibai su 15 zuwa kauyen Liang Jia He, inda Xi ya kasance dalibi mafi karancin shekaru a cikinsu. Liang Yuming, wanda shine sakataren reshen jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a kauyen Liang Jia He a wancan lokaci ya tuna cewa, Xi Jinping na dauke da wata jaka mai cike da littattafai. Liang Yuming ya ce, a waccan rana, sun taimaki daliban daukar kaya, inda akwai wani mazaunin kauyen wanda ke dakon wata karamar jaka, amma a baya yake a kan hanya. Yayin da ake hutu, ya auna jakunkuna na sauran dalibai, inda ya gano cewa, basu kai na karamar jakar nauyi ba. Da suka isa Liang Jia He, an lura cewa, Xi Jinping ya zo da jakunkuna biyu, baya ga waccan karamar jakar, akwai kuma wata jakar fata, wadda ita ma ke cike da littattafai.

Abin da Xi Jinping ya fara burge jama'a shi ne, yana da fari, kana yana da tsayi da siriri.

Akwai gidaje fiye da 60 dake dauke da mutane sama da 200 a kauyen Liang-jia-he, inda wani karamin kogi ya ratsa kauyen, 'yan kauyen kuwa suna zama a gidajen kogon dutse da aka gina a bangarori biyu na kogin. A wajen gidajen kuwa, manyan duwatsu ne kawai. Da rana ta fadi, ana iya ganin hasken fitilu masu amfani da kananzir da suka fito daga tagogin gidajen, fadin sararin kasa da ake iya gani da idanu bai wuce murabba'in mita 100 ba.

Da ganin hakan Xi Jinping ya ce, yanayin "rayuwar mazauna wurin ya yi kama da na kaka-da-kakaninmu a zamanin da can."

An raba daliban 15 cikin kungiyoyi biyu. Wanda ya kunshi Xi Jinping, Dai Ming, Lei Pingsheng, Wang Yansheng, da Yang Jingsheng suna cikin kungiya guda. Kuma sun zauna cikin wani gidan kogon dutse na Zhang Qingyuan, daraktan kungiyar matasa ta JKS dake kauyen na dan wani lokaci.

Daga wancan lokaci, daliban sun fara zamansu a kauyen.

Mazauna kauyen kan zura ido kan daliban da suka zo daga birnin Beijing, daliban ma na zura ido kan mazauna kauyen.

Hakika kallon-kallon da aka yi tsakaninsu ya kasance tsakanin 'yan birni da 'yan kauye, wato tsakanin dalibai da manoma.

Zuwan bikin bazara na shekarar 1969, daliban sun samu damar cin abinci tare da mazauna Yan'an wanda ake samarwa ga baki, wato dage-dage da naman gabas tare da miya mai launin ruwan kasa, soyayyun kaji, dunkulen nama, hakarkarin alade, da barasar shinkafa. A wancan zamanin karancin kayayayyaki, wadannan nau'ikan abinci su ne mafiya daraja, har ma daliban sun yi mamakin cewa, "Ashe yankin Shanbei yana da abinci masu dandano sosai."

Amma bayan jin dadi na dan wani lokaci, an gano ainihin yanayin da kauyen Liang-jia-he ke ciki.

Da zarar ranar 15 ga watan farko bisa kalandar gargajiyar Sin ya wuce, wasu mazauna kauyen sun kulle kofar gidajensu, sun tafi.

A wannan lokaci na kowace shekara, mazauna kauyen kan yi hakan ne bisa dalilan rokon abinci. A gundumar Yanchuan, kusan rabin 'yan kauyuka kan fita waje don rokon abinci, ciki har da wasu shugabannin kungiyoyin kula da shuke-shuke.

Yayin da Xi Jinping ke zantawa da gidan rediyo da talibijin na Yan'an a shekarar 2004, ya waiwayi cewa, wani batun da ya yi wanda ya jawo hankalin mutane a wancan lokaci shi ne, ya baiwa kare burodi. Wato yayin da ya duba jakarsa, ya gano rabin burodi da ya dauko lokacin da ya tashi daga birnin Beijing, wanda ya riga ya lalace, don haka ya bai wa kare. Amma mazauna kauyen basu taba ganin burodi ba, balle ma cinsa. Da suka ji sunan abincin daga bakin Xi Jinping, kuma sun ji yadda Xi Jinping ya yi amfani da shi wajen kiwon kare, lamarin da ya wuce tunaninsu. Hakan ya sa sun ce daliban sun bata abinci, kuma sun yada labarin tsakanin mutane cikin sauri, har ma a karshe dai duk gundumar Yanchuan ta san wannan labarin.

A cikin bayanin da ya rubuta mai taken "Ni 'dan kasa mai launin rawayan ne", Xi Jinping ya waiwayi zaman rayuwarsa a kauyen Liang-Jia-He, inda ya ce, "A lokacin, ni karami ne, kuma ba ni da ra'ayi na dogon lokaci, don haka ban mai da hankali kan batun hadin kai ba. Sauran wadan da ke samun horo a kauyen suna aiki a dutse ko wace rana, amma ni ba haka ba ne, don haka, ban baiwa mazauna wurin wata kykkyawar sura ba."

Kalmar "Hadin kai" da Xi Jinping ya ambata ta fito ne daga koyarwa da mahaifinsa Xi Zhongxun ya ba shi. Xi Jinping ya ce, "Mahaifi na ya kan yi min bayani game da hadin kai, ya kuma bukaci na kasance mutum dake mai da hankali kan hadin kai, da kara karfinmu a fannin, a cewarsa, ana zama tsakanin jama'a, idan an mai da kanka a gaban kome wajen gudanar da ayyuka, to hakan ba daidai ba."

Bisa wannan ra'ayin na "Hadin kai" ne, Xi Jinping ya soma kokarin shigar da kansa a tsakanin jama'a da kauyuka. Saboda daidai wannan ra'ayin na "Hadin kai", sannu a hankali ya fara samun ra'ayi na shiga tsakanin jama'a da hada kai da jama'a. "Iya hada kai da jama'a" wannan ya kasance wani fasalin Xi Jinping wajen bada shugabanci.

Tambar ya zama wani mutum ne na daban, Xi Jinping na kokarin kawar da bambanci a tsakanin yaran birnin Beijing da na kauyen.

Tunkuyau ya kasance abun da ya fi damun Xi Jinping a yayin da yake zama a Liang-Jia-He. Fatar Xi Jinping tana da saukin samun matsala, kuma idan kuma ta cije shi, sa'an nan ya sosa da hannu, wurin da ya sosa zai kumbura. Idan ya kara sosawa sai ya kara yin kaikayi, abun da ya sa Xi Jinping ya sha wahala sosai. Shi Chunyang ya taba aikin gona tare da Xi Jinping a lokacin, ya taba ganin tabon dake kafarsa sakamakon cizon kuma da kwarkwata. Lallai kumburi sun cika kafarsa, wasu sun yi bambarakwai, wasu sun bace sakamakon susa, wasu ma na zubar da jini.

Xi Jinping da sauran dalibai sun nemi hanyoyin tinkarar kuma. Bayan shekaru 2, sai Xi Jinping ya saba, ko da kuwa sun cije shi, yana iya yin barci sosai.

A idannun mazauna kauyen, Xi Jinping ya san abubuwa da dama, kuma da saukin mu'ammala. Kalaman Xi Jinping basu kasance masu haifar da rabuwar kawuna ko na nuna kama karya ba.

Halayyar Xi Jinping ba ta nuna ya fito ne daga birni ba, ya fahimci matasan kauyen cikin sauri. Ya baiwa abokansa dake fama da talauci takalma, a wasu lokuta ya kan yi aski ga matasan kauyen, baya ga haka kuma ya kan koyar wa matasan kauyen wasan iyo. Wani dalibi mai suna Wang Xianping, da wasu 'yan kungiyar jama'a da suka hada da Shu Chunyang, Wu Hui, Zhang Weipang da dai sauransu sun kasance abokansa.

Mazauna kauyen sun riga sun karbi wannan dalibin da ya zo daga Beijing, kana mazauna kauyen sun kara fahimtar wasu wuraren na duniya ta hanyar hira da Xi Jinping.

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v Kauyen Liang-Jia-He(1) 2018-07-01 20:56:23
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China