in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya murnar kaddamar da taron kolin AU karo na 31
2018-07-01 20:54:08 cri
Yau Lahadin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya don taya murnar kaddamar da taron kolin kungiyar AU karo na 31 wanda ke cigaba da gudana a Nouakchott, babban birnin kasar Mauritania, don taya kasashen Afirka murnar shirya taron.

Xi Jinping ya nuna cewa, kungiyar AU tana sa himma wajen inganta yunkurin neman dunkulewar Afirka, kasashen Afirka suna ci gaba da daukar matsayin bai daya kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyya, kana da kara karfinta na kiyaye zaman lafiya da tsaro. Da zuciya daya yana fatan AU za ta ci gaba da jagorantar kasashen Afrika wajen samun sabon cigaba.

Baya ga haka, Xi Jinping ya jaddada cewa, za a shirya taron kolin na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da kasashen Afirka a watan Satumba mai zuwa a nan birnin Beijing. Babban taken taron shi ne "Hada kai don samun nasara tare, kafa kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka". A cewarsa kasar Sin za ta hada kai tare da bangaren Afirka, domin hada kai, da raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" tare, da ajandar neman dawwamamman ci gaban MDD nan da shekarar 2030, da ajandar AU nan da shekarar 2063, da kuma manyan tsare-tsaren kasashe daban daban na Afirka, da nufin ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin bangarorin biyu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China