in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasa da kasa sun yabawa taimakon da kasar Sin ke bayarwa ga cigaban duniya
2018-07-01 17:04:11 cri
Yayin da a yau Lahadi jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) ke cika shekaru 97 da kafuwa, jami'ai da masana na hukumomi daban daban a kasashen duniya suna cigaba da nuna yabo ga irin gudumowar da kasar Sin ke samarwa ga cigaban duniya baki daya.

A bisa alkaluman da hukumar kididdigar ta kasa (NBS) ta fitar a watan Fabrairu game da bayanai kan cigaban tattalin arziki da yanayin zamantakewar al'ummar na shekarar 2017 ya nuna cewa, kasar Sin ta bada gudunmowar kashi 30 bisa 100 ga cigaban tattalin arzikin duniya baki daya ya zuwa shekarar 2017.

A bisa wani rahoton da bankin duniya ya fitar a watan Fabrairu ya nuna cewa, kasar Sin za ta kara shiga a dama da ita wajen samar da dawamamman cigaban duniya, rahoton ya bayyana nasarorin da kasar Sin ta samu na samun bunkasuwa cikin saurin sakamakon shirinta na yaki da fatara kana da yin fice da kasar ta yi cikin sauri.

Yanayin cinikayyar kasar Sin ba wai ya bada gudunmowa ga cigaban duniya kadai ba ne, har ma ya amfanawa kasashen duniya marasa karfi ta hanyar yin muyasar da kasar ta yi na hanyoyin da ta bi wajen cigabanta, kamar yadda Stephen Perry, shugaban kungiyar 48 Group Club, na kasar Birtaniya wanda ya kunshi shugabannin kamfanonin bunkasa cinikayya tsakanin Birtaniya da Sin ya bayyana.

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kana kasa mafi yawan al'umma sama da mutane biliyan 1 da miliyan 300, kasar ta bayar da gagarumar gudunmowa wajen cigaban fannin yawon bude ido na duniya a 'yan shekarun da suka gabata, in ji Zhu Shanzhong, babban daraktan hukumar kula da yawon shakatawa ta duniya.

Ita kuwa mataimakiyar sakatare janar na MDD Amina J. Mohammed, yabawa kasar Sin ta yi game da irin dunbun nasarorin da ta cimma wajen yaki da fatara, a cewarta, nasarorin da kasar Sin ta cimma sun kasance abin koyi ga kasashe masu tasowa a duniya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China