in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dubban mutane na yin bore a fadin Amurka don nuna adawa da tsarin shigi da fici na shugaba Trump
2018-07-01 16:35:39 cri
Dubun dubatar jama'a ne ke ci gaba da yin bore cikin mamakon ruwan sama ko tsananin rana a sassa daban daban na Amurka domin nuna adawarsu da manufofin shugaban kasar Donald Trump game da tsarin dokar shigi da fici na kasar, dokar dai wadda ta yi sanadiyyar raba kananan yara sama da 2,000 da iyayensu wadanda suka tsallaka kasar ta haramtattun hanyoyi.

An yi fama da tsananin rana a tsakiyar birnin Washington D.C. a jiya Asabar, amma duk da haka yanayin bai hana dubban masu zanga zangar cigaba da yin bore ba, wadanda suka taru a babban filin taro na Lafayette Square dake daura da fadar White House.

Masu zanga zangar na yin kiraye kirayen cewa, "Mun damu, a sada iyalai da junansu" wasu kuma na cewa, tsarin dokokin shugaban Amurka Donald Trump game da shigi da fici sun yi tsauri.

Wadanda suka shirya boren sun ce, akwai iyalai sama da 630 daga dukkan sassan kasar da suka yi dandazo a birnin Washington D.C, inda suke yin kiraye kiraye na neman jama'a su fito don nuna adawa da tsare tsaren dokokin shigi da fici na shugaban kasar mai cike da sarkakiya.

Gwamnatin shugaba Trump ta bullo da tsattsauran shiri na ba sani ba sabo game da dokokin da suka shafi bakin haure dake shiga kasar ta Amurka ba bisa ka'ida ba, inda dokar ta nemi a kama sannan a hukunta dukkan wadanda suka shigo kasar ta barauniyar hanya, kana dokar ta nemi a raba iyayen dake tare da 'yayansu, kana a mayar da 'yayan karkashin kulawar sashen kiwon lafiyar al'umma na kasar, inda wasu iyalan na daban za su lura da yaran, da samar musu wurin zama, ko kuma a mayar da su gidajen reno.

A sakamakon tsauraran dokokin, an ga wasu hotunan kananan yaran da aka raba da iyayensu masu tada hankali da suka yi ta yawo a shafukan sadarwa na duniya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China