in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kauyen Liang-Jia-He(1)
2018-07-01 20:56:23 cri

A ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 2015, wato ranar 25 ga watan 12 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, da karfe 11 na rana, motocin bas guda 3 suka tsaya a wajen kauyen Liang-Jia-He. Daga cikin motocin, wasu mutane suka fito, suka tafi cikin kauyen.

"Jinping ya dawo!"

Aka yi ihu, sa'an nan jama'ar kauyen suka fara gudu zuwa kofar kauyen.

Xi Jinping ya koma kauyen Liang-Jia-He, wani karamin kauyen da ke tsakiyar yankin tudun da ake kira "Huang Tu Gao Yuan", wanda ya kasance wani wurin da kullum yake begensa. Zuwa lokacin, shekaru 40 sun wuce tun bayan da ya bar kauyen.

Bayan da ya sa kafa cikin harabar kauyen, inda ya kwashe shekaru 7 yana aiki da zama a wajen, ya yi arba da mutanen kauyen, wadanda ya dade zaune tare da su, kuma har yanzu bai mantawa da su ba, Xi Jinping ya yi farin ciki sosai.

Jama'a sun kewayi Xi Jinping, suna shiga cikin kauyen. Suna tafiya, suna hira.

Bayan da suka isa kofar kwamitin al'ummar kauyen, karin jama'a ne suka isa wajen. Cikin farin ciki suka tsayawa a dab da Xi Jinping, ba wanda ke son bar wurin.

Liang Yuming, tsohon sakataren reshen jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a kauyen Liang-Jia-He, bai samu zuwa da wuri ba, don haka ya yi kokarin shiga cikin jama'a don zama a dab da Xi Jinping. Da Xi Jinping ya gan shi, ya rike hannunsa, ya yi magana da shi cikin murna. Daga bisani, Liang ya ce, "Bari ka yi rangadi, zan koma gida don shirya abinci, an jima kadan sai ka zo gidana don cin abinci."

Xi Jinping ya ci gaba da hira da abokansa mazauna kauyen, inda ya tambaye su, "Ta wane hanya ne suke samun kudin shiga? Mene ne abincinsu na yau da kullum ? Yaya dattawa? Wadanne ayyuka ne yara ke yi? Yaya zaman rayuwarsu? Ana iya samun shinkafa? Ko ana iya samun cin nama kullum? ..."

Abokansa sun amsa cewa, "Yanzu zaman rayuwarmu na da kyau. Kowace rana ana cin gurasa, da fulawa. Ana iya cin shinkafa da nama a duk lokacin da ake so."

Jin haka ya sa Xi Jinping yin murmushi, da nuna gamsuwa, yana mai cewa, "Ya yi kyau, hankalina ya kwanta ganin yadda ku ka samu zaman rayuwa mai kyau"

Xi Jinping ya bar kauyen Liang-Jia-He a shekarar 1975. Sa'an nan a wancan karo, ya zama karo na 2 da ya koma kauyen.

Mazauna kauyen sun tuna cewa, ya koma wajen a karon farko a shekarar 1993.

A ranar 27 ga watan Satumban shekarar 1993, Xi Jinping, wanda a lokacin ke da matsayin mamban zaunannen kwamitin lardin Fujian na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma sakataren kwamitin birnin Fuzhou na jam'iyyar, ya koma kauyen Liang-Jia-He a karonsa na farko.

A Lokacin, Xi Jinping ya ziyarci gidajen mazauna kauyen daya bayan daya, ya kuma tunasar da kowa cewa, "ya kamata a yi kokarin biyan bukatu na samun abinci, gami da na samun ilimi." Ya ba kowane gida wani agogo na lantarki, domin yara su yi amfani da shi yayin da suke karatu. Yana fatan yaran wurin za su samu karin ilimi.

Sa'an nan yayin da ya koma kauyen kafin bikin bazara na gargajiyar kasar Sin na shekarar 2015, ya ware kudi don sayen wasu kayayyakin da jama'a suke bukata a wajen bikin, wadanda suka hada da shinkafa, da fulawa, da man girki, da nama, da hotunan da aka lika kan gefen kofa da bango don taya murnar bikin. Kowane gida ya samu nasa rabon.

An karkata zuwa bakin wani kogi, sa'an nan aka isa farfajiyar da daliban da suka shiga cikin kauyen don samun horo suka taba zama a ciki, inda shi ma Xi Jinping ya yi zama a har fiye da shekaru 5. Gidajen kogon dutse guda 6 a cikin farfajiyar su ne gidajen da jama'ar wurin suka kafa ma daliban a shekarar 1970. Bayan an gama ginasu, Xi Jinping ya fara zama ciki. Bai taba barin wurin ba, har zuwa shekarar 1975.

Bayan da Xi Jinping ya shiga farfajiyar, ya duba kowane gidan kogon dutse. A cikin gidan da ya taba zama, ya yi nuni da hannu ga wani wurin dake karkashin taga, ya ce, "A da, akwai wani dogon teburi mai launin kore a nan. A can gefe ma akwai wani wurin ajiye kaya. Mu kan ajiye akwatunanmu da kayayyakinmu a can."

Tankin iskar gas da a kan samo daga taki dake wajen farfajiar, shi ne tankin iskar gas da a kan samo daga taki na farko a duk fadin lardin Shanxi, wanda mazaunan kauyen Liang-Jia-He suka gina a karkashin jagorancin Xi Jinping. A kan bangon gidan kogon dutse, wato irin gidan gargajiyar wurin dake kusa da tankin, akwai wani zanen da aka yi, inda aka rubuta "Dukufa Wajen Yin Aiki, Dogara Da Kanmu Wajen Zaman Rayuwa" da launin ja. Da Xi Jinping ya ga zanen, ya ce, "Wallahi, zanen na da shekara 40!"

Ya tafi, ya tsaya. Dukkan tsaunuka da mutane na kauyen Liang-Jia-He sun tuna Xi Jinping da abubuwan da suka faru a da.

Akwai wasu gonaki masu kyau da aka kafa karkashin jagorancin Xi Jinping, a lokacin da yake matsayin magatakardan babban reshen jam'iyya na kauyen, har zuwa yanzu, gonakin suna tallafawa al'ummomin dake kauyen Liang-Jia-He.

Xi Jinping ya ce, "A lokacin da muke aikin kafa gonakin, ba mu taba zaton aikin zai ba mu wahala ba, dukkanmu mun yi tsalle cikin ruwan kankara don kafa gonakin." Har cikin wani tsawon lokacin da ya gabata, da aka shiga lokacin sanyi, Xi Jinping na jin ciwo a kafofunsa, wannan shi ne ciwon da ya samu daga aikin kafa gonakin.

A ganin al'ummomin kauyen, har zuwa yanzu, Xi Jinping ya kasance wancen kyakkyawan dalibi mai kokari, mai hakuri, kuma mai son karatu. Bayan shekaru 40, har yanzu irin wannan kyakkyawan halayyar na sa ba su canja ba.

A shekarar 1969, bayan Xi Jinping ya je aiki a kauyen Liang-Jia-He na watanni da dama, Zhang Weipang da diya ta Zhang Guilin sun yi aure. Sabo da gidajensu na da kusa, Xi Jinping da Zhang Weipang suka kulla abota da wuri.

A lokacin, Zhang Weipang ya na fama da talauci sosai, shi ya sa, bayan Xi Jinping ya hau kan matsayin magatakardan babban reshen jam'iyya na kauyen, ya fara ba shi abinci da kansa, har ya ci abinci tare da iyalan Zhang Weipang.

Kuma, kafin Xi Jinping ya je karatu a jami'ar dake birnin Beijing, ya baiwa Zhang Weipang barguna guda biyu, riguna guda biyu har ma da jakarsa ta adana kayayyakin aikin dinkin hannu.

A shekarar 1993, Xi Jinping ya koma kauyen Liang-Jia-He. A lokacin, Zhang Weipang yana noma a kan tsauni, da ya ji labarin dawowar Xi Jinping, ya fara gudu daga saman tsaunin, sa'an nan, ya hadu da Xi Jinping a tsakiyar tsaunin. Zhang Weipang ya ce ,"Da Jinping ya gan ni, ya kama hannuna, muka gaisa, bai ma lura akwai datti sosai a hannu da jikina ba, kuma ban san me zan ce masa ba domin na cika da farin ciki."

Xi Jinping ya taba bayyana cewa, "A lokacin, mutanen wurin sun koya min yadda zan yi zaman rayuwa, yadda zan yi ayyuka, lalle na koyi ilmi da yawa. A lokacin, ni yaro ne mai shekaru 15, ban san komai ba. Amma, daga baya, na koyi yadda ake yin taliya, na iya turara burodi, na iya hada kabeji mai tsami, na iya komai da kome. Ban kara cin kabejin mai tsami cikin lokaci mai tsawo ba, lalle ina son cin."

Xi Jinping bai taba mantawa da dadin kabeji mai tsami na kauyen Liang-Jia-He ba. A ranar 7 ga watan Maris na shekarar 2014, a lokacin da aka gudanar da "taruka biyu", Xi Jinping ya bayyana cewa, "a watan Janairun shekarar 1969, na je aiki a kauye, fararen hula sun taimake ni, sun ba ni abincinsu, idan wani ya ba ni kabeji mai tsami kwano daya, zan ce, yau na kyautata zaman rayuwata. Yanzu da na ga mutanen da suke zama a wuri mai fama da talauci, gaskiya na tausaya musu sosai, a matsayin dan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya kamata mu sa su cikin zukatanmu, mu dukufa domin taimaka musu, in ba haka ba, ta yaya za mu ce muna da tausayi!"

Shekaru 40 da suka gabata bayan ya bar kauyen Liang-Jia-He, kullum Xi Jinping na kula da mazauna wurin.

A shekarar 1994, Lv Housheng ya kamu da cutar kashi ta osteomyelitis a kafar hagu, ya yi jinya a asibiti har tsawon watanni fiye da biyu, inda ya kashe kudin RMB yuan 6000 da wani abu, amma duk da haka bai samu sauki ba, babu sauran dabara, sai Lv wanda ke fama da talauci ya rubuta wasika ga Xi Jinping, don bayyana halin da yake ciki. Bayan 'yan kwanaki, sai Xi Jinping ya turo masa kudi yuan 500 don gayyatarsa zuwa birnin Fuzhou don yin jinya. A yayin da yake Fuzhou, idan Xi Jinping bai yi tafiya ba, ya kan je asibiti kusan ko wace rana da dare, ya kuma gaya masa cewa, "Housheng, ba na la'akari da yawan kudin da zan kashe don samar maka lafiya."

Bayan wasu lokuta, Lv Housheng ya samu sauki, kuma zai koma arewacin Shanxi, sai Xi Jinping ya saya masa tikitin jirgin sama, ya kuma ba shi kudi yuan 2000. Hakan ya burge Lv Housheng sosai, ya ce, "Jinping, ina jin kunya saboda na kashe dubban kudadenka." Xi Jinping ya ce, "Mu abokai ne."

A karshen watan Oktoban shekarar 1999, aka yi wa Lv Housheng tiyata, inda aka yanke masa kafa a birnin Taiyuan. Da Xi Jinping ya samu labari, sai da ya biya dukkan kudin jinya, baya ga haka ya bukaci jami'an wurin su kula da shi. A yayin da Lv Housheng ke ba da lamarin, sai ya nuna bayyana cewa, "Jinping ya min kirki sosai, gaskiya ya damu sosai da ciwon na."

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya taimaka wa kauyen wajen samun wutar lantarki, da gyara makarantu, da gadoji da dai sauransu. Mazauna kauyen ba za su manta da zumunci da kaunar da Xi Jinping ya nuna musu ba. Sun ce, "Zuciyar Jinping tana kauyen Liang-Jia-He."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China