in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta gabatar da takardar bayani mai taken "Sin da kungiyar WTO" karo na farko
2018-06-29 14:30:36 cri

Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da takardar bayani mai taken "Sin da kungiyar WTO" a jiya Alhamis, wannan ne karo na farko da Sin ta gabatar da takardar bayani kan wannan batu. Takardar ta yi nuni da cewa, tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, Sin ta cika alkawarinta da bude kofa ga kasashen waje a fannin kasuwanci. Kana takardar ta tabbatar da cewa, yayin da kasar Sin take bude kofa ga kasashen waje, ba za ta dakatar da alkawarinta da ta yi a lokacin da ta shiga kungiyar WTO ba, sannan za ta ci gaba da fadada bude kofa ga kasashen waje, da kara samar da yanayi mai kyau yayin da take bude kofa a dukkan fannoni.

Takardar bayanin mai taken "Sin da kungiyar WTO", ta kunshi sassan hudu wato Sin ta cika alkawarin da ta yi yayin da ta shiga kungiyar WTO, Sin ta nuna goyon baya ga tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, gudummawar da Sin ta samar wa duniya bayan da ta shiga kungiyar WTO, da kuma yadda Sin ta ke kokarin bude kofa ga kasashen waje.

Takardar ta bayyana cewa, bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO a shekarar 2001, ta kara daidaita ka'idojin cinikinta bisa ga ka'idojin da ke tsakanin bangarori daban daban, ta kuma cika alkawarinta na bude kofarta ga kayayyaki da hidima da aka shigo daga kasashen waje. Mataimakin ministan harkokin ciniki na kasar Sin Wang Shouwen ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, Sin ta cika dukkan alkawarinta a fannin rage harajin kwastam na cinikin kayayyaki a shekarar 2010. Daga baya, Sin ta kara rage yawan harajin da ake biya kan kayayyakin da aka shigar da su. Kana ya zuwa shekarar 2007, Sin ta cika dukkan alkawarinta na bude kofa ga kasashen waje, hukumomin samar da hidima 100 sun bude kofarsu ga kasashen waje bisa alkawarin da aka yi.

Wang Shouwen ya bayyana cewa, "Ban da wannan kuma, muna kokarin cika wasu alkawura a fannonin ikon mallakar fasaha da gudanar da ayyuka a bayyane. A takaice dai, Sin ta yi kokarin cika alkawarin da ta yi yayin da ta shiga kungiyar WTO, kana ta cika su yadda ya kamata. Za mu ci gaba da daukar alhakinmu, tare da fatan sauran membobin kungiyar WTO za su cika alkawarinsu yadda ya kamata."

A cikin shekaru 17 da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, rayuwar jama'ar Sinawa ta inganta, an kuma samu bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, kana Sin ta kara hada kan da sauran kasashen duniya wajen samun moriyar juna. Wang Shouwen ya bayyana cewa, Sin ta soke kashi 97 cikin dari na haraji da ake biya kan wasu kasashen da ba su ci gaba ba da suka kulla dangantakar diplomasiyya tare da kasar Sin, don haka Sin ta zama kasuwa mafi girma da irin wadannan kasashe suka shigo da kayayyaki cikin kasar. Haka kuma Sin ta yi hakan ga kasashe mafi ci gaban tattalin arziki a duniya, Wang Shouwen ya bayyana cewa,

"Tun daga shekarar 2008 zuwa 2017, kayayyakin da kasar Amurka ta fitar zuwa kasar Sin ya karu da kashi 86 cikin dari, amma a wannan lokaci, yawan kayayyakin da kasar Amurka ta fitar zuwa sauran kasashen duniya ya karu da kashi 21 cikin dari ne kawai. Game da samar da hidima, tun daga shekarar 2007 zuwa 2016, yawan hidimar da kasar Amurka ta samar wa kasar Sin ya karu da ninki uku, amma yawan hidimar da Amurka ta samarwa sauran kasashen duniya ya karu da kashi 50 cikin dari."

Ban da wannan kuma, takardar ta yi nuni da cewa, yayin da kasar Sin take bude kofa ga kasashen waje, ba za ta ci gaba da cika alkawarin da ta yi lokacin da ta shiga kungiyar WTO. Ya kamata Sin ta tunkari canje-canje da bunkasuwar da aka samu a duniya, da fadada bude kofa ga kasashen waje, da kara matakan bude kofa a dukkan fannoni don samun moriyar juna.

Hakazalika kuma, tadarkar ta bayyana cewa, bayan da Sin ta shiga kungiyar WTO, Sin ta nuna goyon baya ga tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, da shiga ayyukan kungiyar WTO a dukkan fannoni, da sa kaimi ga kungiyar WTO da ta kara dora muhimmanci ga batutuwan da suka shafi membobin kungiyar, da yaki da ra'ayin bangaranci da ra'ayin ba da kariyar ciniki, da tabbatar da ikon tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban. Wang ya bayyana cewa,

"Sin za ta hada kai tare da sauran membobin kungiyar WTO wajen kyautata ka'idojin ciniki a tsakanin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kungiyar WTO bisa yanayin da ake ciki. Sin tana goyon bayan tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban kamar yadda doka ta tanada, da sa kaimi ga bunkasuwar tsarin tattalin arzikin duniya na bai daya mai bude kofa da samun moriyar juna da daidaito."(Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China