in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WTO ta yi maraba da kudurin Sin na goyon bayan tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa
2018-06-29 11:04:41 cri

Hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO, ta yi maraba da wani kuduri da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar a karon farko mai taken "kasar Sin da hukumar WTO".

Jami'an cinikayya sun ce, kudurin ya bayyana goyon bayan kasar Sin ga tsarin cinikayyar kasa da kasa, wanda WTO ke sanyawa ido. Inda suka ce za su jira a wallafa shi cikin tsarukan hukumar tare da raba shi tsakaninsu.

Kakakin hukumar Keith Rockwell, ya ce har kullum, sakatariyar WTO, na maraba da irin goyon bayan da kasar Sin ke ba hukumar.

Ya ce, kasar Sin na shiga cikin dukkan harkokin kungiyar, kuma a bayyane ya ke cewa, damawar da ake da kasar Sin ta taka muhimmyar rawa ga nasarar cimma yarjejeniyar rage shingayen cinikayya ta TFA da kuma yarjejeniyar cinikayya da aka cimma tsakanin wasu kasashe wadda ya fadada yarjejeniyar amfani da fasahar sadarwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China