in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya dandalin tattaunawa kan bunkasa shirye-shiryen talabijin na zamani na Afirka a Beijing
2018-06-29 10:41:52 cri

Jiya Alhamis ne a birnin Beijing, aka kaddamar da dandalin tattaunawa kan bunkasa shirye-shiryen talabijin na zamani karo na 8. Shugabannin hukumomin talabijin da rediyo na kasashen Afirka 43, gami da na kasashen Asiya guda biyar, tare kuma da wakilai daga bangarorin siyasa da tattalin arziki da kafofin watsa labarai na kasar Sin su sama da dari hudu ne suka hallara, inda suka yi musanyar ra'ayoyi dangane da yadda za'a yi kokarin habaka harkokin sadarwar zamani a Afirka, da samar da wata kyakkyawar alkibla ga hadin-gwiwar kafofin watsa labaran Sin da Afirka.

A yayin bikin kaddamar da taron, mataimakin darektan ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Guo Weimin ya ce, kafofin watsa labarai wata muhimmiyar gada ce dake iya karfafa zumunci da mu'amalar al'adu tsakanin jama'ar Sin da Afirka. Guo na da imanin cewa, wannan dandalin zai taimaka matuka ga raya shirye-shiryen talabijin na zamani na Afirka, ta yadda zai samar da alfanu ga jama'ar Afirka baki daya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China