in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ya kashe adadin kudin da bai taba kashewa ba wajen sayen kayakin agajin ga yara a 2017
2018-06-29 09:43:36 cri
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya ce ya kashe sama da dala miliyan 500 wajen sayen kayayyakin bukatun gaggawa na yara a 2017, adadin da bai taba kashewa ba.

UNICEF ya ce an kashe kudin ne a lokacin da rashin abinci da fari da rikici da rashin sinadaran gina jiki ke barazana ga rayuwa miliyoyin yara, musammam a kasashen Sudan ta Kudu da Yemen da Somalia da arewa maso gabashin Nijeriya.

Baya ga abubuwan da suka danganci gina jiki, UNICEF ya aike da ruwan sha da kayayyakin tsaftar muhalli da allurran riga kafi da magunguna da kayakin karatu da suturu, ga yara da iyalan dake yankunan dake fama da rikici, ko kuma suke gudun hijira saboda rikici ko aukuwar wani iftila'i da sauran wasu matsaloli a kasashe 61.

A takaice, UNCEF ya samar da kayayyaki da hidimomi da darajarsu ta kai dala biliyan 3.46 ga yara a kasashe da yankuna 150.

Bugu da kari, UNICEF da abokan huldarta, sun rage farashin alluarar riga kafi a shekarar 2017, inda ake samun jerin allurran riga kafi ga yara 'yan kasa da shekara 1 a kan farashi kasa da dala 18 a kasashen da ba su da karfin tattalin arziki, farashin da ya yi kasa daga dala 24.46 a shekarar 2013. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China