in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fara aikin gina tashar samar da wutar lantarki mafi girma a Zimbabwe
2018-06-28 14:05:01 cri

 


 

A jiya Laraba ne, aka fara aikin inganta injunan samar da wutar lantarki ta karfin kwal na Hwange, wanda ya kasance irin aiki mafi girma da Sin ta gudana a Zimbabwe, kuma aikin samar da ababen more rayuwa ta fuskar makamashi mafi girma tun bayan da Zimbabwe ta samu 'yancin kanta. Wannan aiki dai zai taimakawa Zimbabwe wajen magance matsalar karancin wutar lantarki da take fama da shi.

A jiya Laraba 27 ga wata ne, shugaban kasar Zimbabawe Emmerson Mnangagwa da daukacin masu ruwa da tsaki na Sin da Zimbabwe suka halarci bikin kaddamar da aikin inganta injunan samar da wutar lantarki na Kwange, aikin da ake saran kammala shi cikin watanni 42. Ana kuma saran aikin zai lashe kudin da ya kai kusan dala biliyan 1.5. Bankin shige da fice na Sin ne ya samar da rancen dala biliyan 1 don gudanar da wannan aiki. Wannan aiki na daya daga cikin ci gaban da ziyarar Mnangagwa ya samu a yayin da ya kawo ziyara a kasar Sin a farkon watan Afrilu na bana, bankin ya fara samar da rancen kudin ne tun a watan Mayu, yanzu an riga an samar da kashin farko na kudi wato dala miliyan 200.

A jawabin da shugaban ya gabatar a yayin bikin kadammar da aikin, ya bayyana godiya sosai ga kasar Sin, ya ce:

"Ina fatan ma'aikatan kamfanin samar da wutar lantarki na Zimbabwe da kamfanin Sinohydro za su yi kokarin kammala wannan aiki a kan lokaci. Hadin kan dake tsakaninsu ya bayyana dankon zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen biyu."

Tashar Hwange dake da nisan kilomita 800 daga Harare, ta kasance tashar samar da wutar lantarki bisa karfin kwal mafi girma a kasar, wanda ke da injuna guda 6 dake iya samar da kilo waz dubu 920 na wutar lantarki, amma saboda rashin gyara, tashar na samar kimanin kilo waz dubu 500 na wutar lantarki ne kawai. Alkaluman kididdigar hukumar makamashi ta kasar sun nuna cewa, yawan wutar lantarki da Zimbabwe ke iya samarwa ya kai kilo waz miliyan 2.2, amma yanzu kilo waz miliyan 1.2 ake samarwa kawai, yawan bukatun kasar ya kai kilo waz miliyan 1.6, don haka akwai babba gibi kwarai da gaske.

Manajan darektan kamfanin Sinohydro dake kula da wannan aiki Mista Liang Jun ya ce, kamfanin zai kara injuna biyu, kuma ko wanensu zai iya samar da kilo waz dubu 335 na wutar lantarki, matakin da zai magance karancin wutar lantarkin da ake fuskanta yanzu haka a kasar, kuma kayayyakin zamani da kamfanin ke amfani da shi zai taimakawa Zimbabawe wajen kiyaye muhalli. Ya ce:

"Bayan an kammala wannan aiki a shekarar 2022, zai taimaka wajen raga matsalar karancin wutar lantarki da Zimbabwe ke fuskanta, a sa'i daya kuma, muna yin amfani da wasu matakan kimiya da fasaha na zamani, matakin da zai taimaka wajen kyautata tsarin wutar lantarki na Zimbabwe, ta yadda za a yi tsimin makamashi da kiyaye muhalli."

Rahotanni na cewa, a watan Oktomba na shekarar 2014, kamfanin samar da wutar lantarki na Zimbabwe ya sa hannu kan wata kwangilar EPC da kamfnain Sinohydro, a cewar Mista Liang, kamfani zai dauki kwararan matakai a wannan aiki. Ya ce:

"Kamfaninmu zai gina da kuma rika kula da aikin. Matakin da zai amfana wajen fitar da kudi da kimiyyar Sin zuwa kasashen waje, kuma zai taimakawa kamfanonin wurin wajen daga karfin kula da harkoki da yin amfani da kimiya da fasaha, ta yadda Zimbabwe za ta iya kara karfinta na raya tattalin arzikinta. Ban da wanna kuma matakin zai iya kawo moriyar juna da bunkasar Sin da Afrika bai daya da kuma zama abin koyi ga hadin kan Sin da Afrika."

Jakadan Sin dake Zimbabwe Mista Huang Ping ya nuna kyakkyawar fata ga aikin da ake gudanarwa a Hwange. Ya ce, wannan shekara na da muhimmanci matuka ga dangantakar kasashen biyu, shugaba Mnangagwa ya kai ziyara a kasar Sin, abin da ya daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, matakin da zai amfanawa jama'ar kasashen biyu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China