in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane fiye da 200 sun mutu a sakamakon harin da aka kai a kauyukan dake tsakiyar Nijeriya
2018-06-28 11:07:00 cri
Dan majalisar dokokin jihar Plateau ta kasar Nijeriya Peter Gyedeng ya bayyana cewa, mutane fiye da 200 ne suka mutu a sakamakon harin da aka kai kan kauyuka 11 na jihar dake tsakiyar kasar Nijeriya.

Wannan jami'i ya bayyana cewa, dakaru sun kai hari ga kauyuka 11 dake jihar Plateau a daren ranar 23 ga wata. A halin yanzu, yawan mutane da suka mutu a sakamakon harin ya haura 200, kuma adadin zai iya ci gaba da karuwa.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a cikin kauyuka 11 da aka kaiwa harin, yawan mutanen da suka mutu a kauyen Ruku ya zarce 47. Banda salwantar rayuka da raunatar mutane, harin ya kuma lalata wasu gine-gine da motoci. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China