in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Amurka
2018-06-27 19:39:56 cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan tsaron kasar, janar Wei Fenghe, ya gana da ministan tsaron kasar Amurka James N. Mattis a yau Laraba, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A wajen ganawar, janar Wei ya ce, tilas ne kasashen Sin da Amurka su tsaya kan magance arangama da juna, da mutunta juna, da kokarin gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za su iya samun ci gaba tare. A nasa bangaren, Mista Mattis na kasar Amurka ya ce, ci gaban kasar Sin zai haifar da moriya ga kasar Amurka, gami da daukacin duniya baki daya, don haka ya kamata kasashen 2 su zama cikin jituwa. A cewarsa, kasar Amurka ta dora muhimmanci kan huldar dake tsakanin sojojin kasashen 2, wadda ke son kara kyautata tsarin musayar ra'ayi da kasar Sin.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China