in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban darektan NTA ya yaba da hadin gwiwar Sin da Afirka wajen raya kafofin watsa labarai
2018-06-27 14:10:41 cri

Bayan shekaru 6 da gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kafofin yada labarai na Sin da Afirka, kafofin yada labarai na Sin da Afirka sun ci gaba da karfafa hadin gwiwarsu domin raya mu'amalar al'adu dake tsakanin al'ummomin bangarorin biyu, da kuma habaka musayar ra'ayoyi kan harkokin manufofin tafiyar da ayyukansu, kara yada labarai da kuma ra'aya sana'o'in da abin ya shafa da dai sauransu, inda kuma aka cimma sakamako da dama. Musamman ma a fannin watsa da shirye-shiryen kafofin watsa labarai dake cikin "Shirin Johannesburg na taron FOCAC tsakanin shekarar 2016 zuwa shekarar 2018", ta yadda zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare.

A jawabinsa yayin taron dandalin tattaunawar hadin kai ta fuskar yada labarai karo na 4 da ya gudana jiya a nan birnin Beijing, mataimakin ministan yada labarai na kasar Sin Nie Chenxi ya bayyana cewa, ya kamata a daga matsayin hadin gwiwar kafofin yada labarai na Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi a fannoni guda uku domin kara tallafawa al'ummomin Sin da Afirka. Yana mai cewa, "Da farko, a karfafa mu'amalar manufofin kafofin yada labarai, domin zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. Ya kamata hukumomin gwamnatocin Sin da Afirka su kara yin mu'amalar a tsakaninsu kan manufofin kafofin yada labarai, domin neman hanyar da za ta dace da bunkasuwar harkokin yada labarai na kasashe masu tasowa, da kuma samar da damammaki masu kyau ga kafofin yada labarai na Sin da Afirka wajen neman sabbin ci gaba da kuma zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata."

"Sa'an nan kuma, a kara yin ma'amala a tsakanin kafofin yada labarai domin karfafa 'yancin Sin da Afirka a fannin yada labarai tsakanin kasa da kasa. Muddin, Sin da Afirka suka yi hadin gwiwa da mu'amala kan harkokin yada labarai, za su iya taimakawa juna wajen bayyana ra'ayoyinsu yadda ya kamata cikin harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da zurfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin bangarorin biyu da kuma hadin gwiwar dake tsakaninsu."

"A karshe, ya kamata a raya fasahohin zamani na kafofin yada labaran Sin da Afirka, ta yadda za a inganta wannan aiki. A 'yan shekarun nan, kasar Sin ta dukufa wajen kyautata tsarin kafofin yada labarai, bisa bunkasuwar fasahohin sadarwa, kuma wasu kasashen Afirka, sun samu ci gaba a wannan fanni, ya kamata Sin da Afirka su kara bullo da shirye-shiryen yin hadin gwiwa domin kyautata tsarin kafofin yada labarai da kuma fuskantar kalubalolin da abin ya shafa yadda ya kamata."

Haka kuma, a yayin da yake halartar taron dandalin tattaunawar hadin kai ta fuskar yada labarai karo na 4 da aka yi a nan birnin Beijing a jiya Talata, babban darektan gidan talabijin na Najeriya NTA Yakubu Ibn Mohammed ya bayyana ra'ayoyinsa kan ci gaban Sin da Nijeriya suka samu a fanni kafofin yada labarai, yana mai cewa, "An samu ci gaba sosai, idan kin duba daga lokacin da aka fara, shekara da shekaru da suka wuce tun zamanin da a lokacin da ake daukar labarin inda a wancan lokacin mutum ne zai hau kan doki a bashi wasika daga wani wuri ya kai wani wuri, daga baya aka zo aka canza aka samu waya da sauransu, to yanzu kuma an samu ci gaba bayan wayar da sauransu, a yanzu kuma an koma amfani da intanet, abin da a hausance ake kira da hanyar yanar gizo, saboda haka yanzu ci gaban ma ya wuce wannan, da akwai abin da ake kiransa a turance "digitalization", wato yanar gizo a hausance, to amma a yanzu ya dara abin da aka sani ta hanyar yanar gizon, ya dara shi kadan, to yanzu haka a Najeriya abin da ake kokawa a kansa ke nan. Na san a kasar Sin dai an riga an kai wannan matsayin tun tuni, yanzu a Najeriya ana nan ana fama har an fara cimma nasara, in sha Allah daga nan zuwa wani lokaci bada jimawa ba duk harkokin talabijin a Najeriya zasu kai wannan matsayin, ta hanyar yanar gizo amma mafi daraja."

Bugu da kari, ya ce, idan muna son ci gaba da raya wannan aiki, baya ga goyon baya na fasahohi da kudade, ya kamata mu ilmantar da mutane kan wannan aiki, ya ce, "Bayan wadannan abubuwa, abin da ya fi muhimmanci shi ne ilmi, komai kudinka, komai kayan aikinka, idan baka karanci wannan fannin ba to ka yi aikin banza, saboda haka, idan an samu kudi da kayan aiki, sai kuma a hada da ilmin wannan aikin da ake son yi, to kuma kasar Sin za ta iya taimakawa Najeriya sosai wajen ilmantar da ma'aikata ta wannan fannin na aikin talabijin."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China