in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta lashi takobin yaki da miyagun kwayoyi
2018-06-27 11:42:51 cri
Fadar shugaban kasar Sudan ta bayyana kudurinta na taimakawa kamfel din da ake yi game da yaki da miyagun kwayoyi a kasar.

Mataimakin shugaban kasar Hassabo Mohamed Abdul-Rahman wanda ya sanar da hakan jiya Talata yayin da yake jawabi albarkacin bikin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta duniya, ya kuma nanata kudurin gwamnati na ganin an dakile amfani da kuma yaduwar miyagun kwayoyi a fadin kasar.

Ya kuma umarci ma'aikatar ilimin kasar da ta kebe wasu azuzuwa a dukkan makarantun kasar don ilimantar da dalibai game da illar da miyagun kwayoyi suke haifarwa, kana a kara gudanar da bincike da nazari game da daililan dake sa mutane ta'ammali da miyagun kwayoyin da kuma yadda kwamitin yaki da miyagun kwayoyin kasar zai kula da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma yi kira ga ma'aikatar kiwon lafiyar kasar, da ta kara samar da cibiyoyin tsugunar da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi, su kuma samar da kulawar lafiya ta musamman yayin kula da irin wadannan mutane.

Shi ma da yake jawabi ministan harkokin cikin gidan kasar Ibarhim Mahamoud Hamid, ya ce kasarsa na shirin kulla yarjejeniya da kasashe makwabta domin karfafa matakan yaki da miyagun kwayoyin.

Alkaluma na nuna cewa, Sudan na zama zangon safarar nau'o'in miyagun kwayoyin saboda kusancinta da manyan kasashe da dama, lamarin da ya kara haifar da matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China