Cikin sakon da ya aike albarkacin ranar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta duniya da aka yi bikinta a jiya Talata, babban sakataren MDDr ya ce kalubalen miyagun kwayoyi na daga cikin matsaloli masu sarkakiya da duniya ke fuskanta a halin yanzu, lamarin dake yin mummunan tasiri ga lafiyar bil-Adama, iyalai, al'ummomi da tsaro da samun ci gaba mai dorewa.
Ya ce, muddin ana bukatar magance wadannan matsaloli, wajibi ne a dauki matakai daban-daban, kamar yadda ya ke kunshi cikin sakamakon muhimman bayanan da babban taron MDD na musamman da ya gudana a shekarar 2016 game da matsalar miyagun kwayoyi a duniya ya amince da shi bai daya
Jami'in na MDD ya ce, baya ga hadin gwiwar kasa da kasa da amfani da managartan dokoki, akwai bukatar a fafada matakai na zahiri kan yadda za a kare, a magance, a kuma bada taimako don a kawo karshen wannan matsala.(Ibrahim)