in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban mai horas da 'yan wasan Najeriya yace saura kiris su kai labari
2018-06-27 11:11:29 cri
Kocin dake horas da tawagar 'yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya zargi tawagar 'yan wasansa da rashin kwarewa wajen kasa tsallakawa mataki na gaba a gasar cin kofin duniya a wasan da suka buga da Argentina a daren jiya Talata.

Najeriyar dai ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Argentina a wasan da aka buga a filin wasa na Saint Petersburg, inda aka zara musu kwallo bayan da aka kai mintoci 87 da fara wasan. Ita kuwa Croatia ta samu nasarar tsallakawa mataki na gaba bayan ta doke Iceland da ci 2-1 a wasan da suka buga a rukunin D, wannan sakamako ya tabbatar da cewa a halin yanzu an cire Najeriyar a gasar.

"Wannan babban abin takaici ne saboda kungiyata ta yi matukar taka rawar gani a gasar," Rohr ya fadawa 'yan jaridu jim kadan bayan kammala gasar. "Wasu 'yan mintoci ne kadan suka rage mana mu tsallake wannan zagaye."

"Tawagar matasan 'yan wasana sun kasa gane yadda ake tafiyar da mintocin karshe na gasa. Ina alfahari da 'yan wasana. Amma dole ne mu karbi wannan sakamako" ya fadi hakan ne a taron manema labarai bayan kammala gasar.

Bayan data samu wannan nasara, a yanzu Argentina ta zo ta biyu a rukunin D inda zata nemi shiga zagaye na 16, inda zata fafata da Faransa. Rohr ya taya abokan karawar tasu murna kana ya musu fatan cigaba da murza leda a gasar cin kofin duniyar dake gudana.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China