in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da dandalin tattaunawar hadin kai ta fuskar yada labarai karo na hudu a Beijing
2018-06-27 10:14:18 cri
A jiya ne aka bude taron dandalin tattaunawar hadin kai ta fuskar yada labarai karo na 4 a Beijing, inda kafofin yada labarai na Sin da Afrika suka sa hannu kan yarjejeniyar hada kai 12, tare da zartas da sanarwar zurfafa hadin kai da mu'ammala tsakaninsu.

A jawabinsa yayin bude taron, mataimakin ministan yada labarai na kasar Sin Nie Chenxi ya bayyana cewa, kamata ya yi, Sin da Afrika su ci gaba da martaba ka'idar nuna adalci ga juna da hada kai da kawo moriyar juna, da bunkasa hadin kai a sha'anin yada labarai zuwa wani sabon matsayi ta hanyar mu'ammala da musaya a fannin kafofin yada labarai, da kara hadin kan ayyukan yada labarai, ta yadda jama'ar bangarorin biyu za su amfana da taka rawa wajen inganta rayuwar Bil Adam.

Rahotanni na cewa, bisa hadaddiyar sanarwar zurfafa hadin kai na dandalin, bangarorin biyu sun yanke shawarar yin amfani da zarafi mai kyau na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika da za a gudanar a watan Satumba mai zuwa, don kara zurfafa hadin kansu karkashin ka'idojin dandali ta hanyoyi biyar, wato yin mu'ammalar manufofi, kara hadin kai a wasu muhimman fannoni na yada labarai, goyawa juna baya kan wasu manyan batutuwan duniya, da cimma matsaya guda a fannin da dai sauransu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China