in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara yin hadin gwiwa da kasashe daban daban don kau da miyagun kwayoyi
2018-06-26 19:54:56 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya furta a wajen wani taron manema labaru na rana rana da ya gudana a yau Talata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan aikin dakile ta'ammali da miyagun kwayoyi, kana tana kokarin taimakawa ayyukan kau da shan kwayoyi masu cutarwa da ake gudanarwa a kasashe daban daban, gami da halartar ayyukan hadin gwiwa a wannan fanni. Ya ce kasar ta Sin ta riga ta kulla yarjejeniyar kau da miyagun kwayoyi tare da kasashe da dama, haka kuma ta tallafawa kasashe makwabta wajen gudanar da aikin yaki da miyagun kwayoyi. A nan gaba, in ji kakakin, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin hadin gwiwa da kasashe daban daban, don neman samar da wata duniya "maras miyagun kwayoyi". (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China