in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Chadi ya gana da babban jami'in kasar Sin
2018-06-26 11:12:02 cri

Jiya ne shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya gana da tawagar kasar Sin karkashin jagorancin Mista Chen Min'er, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma daraktan reshen jam'iyyar da ke birnin Chongqing a N'Djamena hedkwatar kasar.

Yayin ganawar tasu, Mista Chen ya nuna cewa, shugabannin Sin da Chadi sun taba ganawa da juna sau da yawa a shekarun baya-bayan nan, inda suka yi musanyar ra'ayi kan zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni daban-daban, ta yadda za a daga matsayin dangantakarsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, shugaba Deby ya bayyana cewa, Chadi na yabawa sosai kan ci gaban da Sin take samu wajen aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje, kuma yana godiya sosai kan tallafi da taimakon da Sin take baiwa kasarsa ta fuskar raya tattalin arziki da al'ummar kasar.

Ya ce, yana sa ran halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika da za a gudanar a watan Satumba na bana a Beijing, domin tattauna da bangarori daban daban kan yadda za a inganta hadin gwiwa tsakanin Afrika da Sin. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China