in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Larabawa sun tattauana game da karfafa hulda da kasar Sin gabanin taron ministoci da za a yi a Beijing
2018-06-26 11:04:04 cri

Kamfanin dillancin labarai na Masar MENA, ya ruwaito cewa, Kasashen Larabawa sun gudanar da taro don tattaunawa game da hanyoyin karfafa huldarsu da kasar Sin a fannoni da dama da suka hada da zaman lafiya da tsaro da musayar al'adu.

Taron da ya gudana jiya Litinin a hedkawatar kungiyar kawancen kasashen Larabawa, na da nufin shiryawa taron ministoci karo na 8, na dandalin tattaunawar hadin kan kasashen Larabawa da kasar Sin, da zai gudana ranar 10 ga watan Yuli a nan birnin Beijing.

Taron wanda ya samu halartar wakilan din-din-din na kasashen Larabawa a kungiyar, ya tattauna kan yadda za a samar da hadin gwiwa da ta shafi dukkan bangarori, tsakanin kasashen da kasar Sin, bisa shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta kasar Sin.

Shawarar na da nufin gina hanyar cinikayya da ababen more rayuwa, da suka hada nahiyar Asiya da Afrika da Turai a kan hanyar Siliki ta da. Yankin Gabas ta taskiya na taka muhimmiyar rawa cikin shawarar, kasancewarta matsayin gadar da ta hada Sin da Afrika da kuma Turai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China