Da yake ganawa da manema labarai kafin wani taron neman tallafi da ya gudana jiya, wanda kwamitin wucin gadi na babban zauren MDD ya shirya, shugaban hukumar Pierre Krahenbuhl ya nemi kasashe mambobin majalisar su ba da tallafi mai yawa.
Hukumar UNRWA a takaice, ta shiga wannan shekarar ne da gibin dala miliyan 146.
Yanayin da take ciki ya kara tabarbarewa ne bayan gwamnatin Amurka ta zaftare dala miliyan 300 daga cikin tallafin da take ba hukumar. Amurka ta kasance kasa mafi tallafawa hukumar cikin gomman shekaru da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)