in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda kasar Sin ta kasance gagara ba dau
2018-06-26 10:57:40 cri

A kwanakin baya ne, wata 'yar jarida daga tarayyar Najeriya mai suna Funke Egbemode ta kawo ziyara kasar Sin, wadda ta kasance ziyara ta biyu ta 'yar jaridar ta kawo kasar ta Sin cikin shekaru biyu.

Bayan ta koma gida Najeriya ne, 'yar jaridar ta rubuta wani sharhi game da ci gaban kasar Sin, da ma yadda kasar Sin ta kasance gagara ba dau a fannonin ci gaba idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya.

Funke ta fara ne da cewa, Allah ya halicci mutane da siffofi dabam-dabam, wasu dogaye, wasu gajeru, wasu masu basira fiye da wasu, haka kuma wasu bakake wasu kuma farare, sannan ya ajiye kowanne a wurin da yake ganin ya dace da shi. Amma duk da haka ita mai kishin kasarta Najeriya ce a duk inda ta samu kanta.

Ta ce, ta ziyarci kasar Sin a shekarar da ta gabata, bayan wancan ziyara ta koma gida da tarin tambayoyi. Haka kuma a wannan shekara da muke ciki, 'yar jaridar ta sake kawo ziyara kasar Sin, amma wannan karon wata muhimmiyar tambaya ta dawo da ita: shin wai kwakwalwar Sinawa ta sha bamban da ta sauran mutane a duniya ne? Ko sun fi kowa dabara da kwarewa ne? Sannan me ya sa kasar Sin ta ke da girma da kyan gani a fannonin dabam-dabam, yayin da Najeriya ke fadi tashi a wasu kananan fannoni? Me ya sa kasar Sin take samun ci gaba cikin sauri haka?

Yayin da ta kewaya lungu da sakon kasar Sin kuwa, 'yar jaridar ta ce, ta yi tafiya a mota har kusan sa'o'i 18 ba tare da samun rami a kan hanya ba. Ta ce ta ga manyan hanyoyi ta ko'ina, an gyara bishiyoyi da furanni abin sha'awa. Haka kuma hanyoyin karkashin kasa an gina su da inganci. Ga kananan motoci da babura masu aiki da wutar lantarki ta ko'ina.

A dukkan biranen kasar Sin da ta ziyarta, an shuka bishiyoyi da furanni, sannan masu kula da wadannan shuke-shuke sun himmatu wajen kula da su ba dare ba rana kamar 'yayan da suka haifa. Har ma sun tsaya suka dauki hoton wasu ma'aikatan dake kula da irin wadannan furanni a Zhuhai.

'Yar jaridar ta ce, kamar yadda Sinawa suka dukufa wajen kula da irin wadannan bishiyoyi, haka suke mayar da hankali wajen raya muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a. Ga dogayen gine-gine masu siffofi da launuka daban-dabam kamar za su taba sararin samaniya. Wasu gine-ginen ma sun kai hawa 50 zuwa 70, kuma idan dare ya yi ne za ka kalli kwarewar Sinawa a wannan fanni, Garuruwa da dare kamar bishiyoyin bikin kirsimeti inda za ka wuta masu launuka iri-iri sun kawata harabar gine-gine.

Gini na biyu mafi girma a duniya yana birnin Shanghai ne na kasar Sin, yana da hawa 118, ta ce a lokacin da suka ziyarci birnin sun je har hawa na karshe na wannan gini cikin kasa da minti 1.

Ta ce, sun shiga jirgin kasa mai saurin tafiya ne a lokacin da suka je birnin na Shanghai, inda suka yi tafiyar kilomita 1,318 cikin sa'o'i 4 da mintuna 30, jirgin yana gudun kilomita 330 ne cikin kowane sa'a, wato kamar tafiya daga Lagos zuwa Maiduguri, nisan kimanin kilomita 1,227. Haka kuma tashoshin jiragen kasa dake biranen Shanghai da Beijing, fadar mulkin kasar Sin sun fi filin jirgin saman Najeriya girma.

Abin tambaya a nan shi ne, me ya sa babu jiragen kasa na zamani a Najeriya, da mutane za su yi tafiya mai nisa kamar suna cikin dakunansu? Ba wai maganar jiragen kasa masu saurin tafiya ba, ko da jirage na yau da kullum za su biya bukatun jama'a. Da filayen jiragen kasa na zamani, masu tsafta da ban sha'awa. Me ya sa shugabanni da 'yan siyasar kasar Sin suka yi zurfin tunanin samar da tsarin sufurin da zai biya bukatun al'ummominsu? Ta yaya suka yi tunanin cewa, yadda yawan al'ummarsu ke karuwa, akwai bukatar canjawa daga tsohon tsarin jiragen kasa zuwa jiragen kasa na zamani masu saurin tafiya? Amma har yanzu kasashenmu na nan gwamma jiya da yau.

'Yar jaridar ta kara cewa, yaya ake manyan gine-gine a kasar Sin a kowace shekara kamar shuka bishiyoyi, yayin mu kuma mun kasa kula da wadanda muka gada? Sannan ba a maganar wadanda ke Abuja, babban birnin kasar. Ofisoshin gwamnati ba wurare ne na neman riba ba, ma'aikata na dandana kudarsu saboda matsalar sufuri.

Baya ga batutuwan dogayen gine-gine, da jiragen kasa masu saurin tafiya, akwai bukatar mutum ya kalli birnin nan na Shenzhen. Shekaru 39 da suka gabata, 'dan karamin gari ne na kamun kifi da ake kira Bao'an, mai yawan al'umma 30,000, masunta masu sayar da kifi. Kuma babbar hanya daya ce a garin da tsohuwar hanyar da ta hade kananan hanyoyin da suka shiga garin. 'Yan shaguna da dakunan cin abincin sun kara kawata garin na Bao'an da ake kira Shenzhen a yau, birnin da ya canja cikin kasa da shekaru 20 daga wani karamin kauye zuwa babban yankin masana'antu da kasuwanci a taswirar duniya.

An yi kiyasin cewa, a shekarar 2008, yawan al'umma ya karu zuwa miliyan 12, inda jama'a suka kaura daga dukkan sassan duniya, suke kuma harkokinsu na kasuwanci a lungu da sako daban-dabam.(Yaya Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China