in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya bukaci kwamiti sulhun MDD ya tunkari rikicin Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika
2018-06-26 10:01:02 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bukaci kwamitin sulhun MDD da ya yi kokarin amfani da hanyoyin sasanto wajen warware kalubalolin tsaro dake addabar yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika.

Jami'in MDDr ya yi wannan kiran ne a lokacin wata mahawara wadda kwamitin ya gabatar, wanda ta mayar da hankali kan batutuwa da suka shafi yankunan.

Ya ce, sassan yankuna a kasashe kamar Syria, Yemen da Libya suna cikin barazana. Ana tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu. Kuma tasirin wadannan tashe tashen hankula ya bazu zuwa kasashen dake makwabtaka da su har ma ya zarta hakan.

Babban jami'in MDDr ya sake ankarar da kwamitin sulhun game da dunbun matsalolin rikice rikice da suka dabaibaye yankunan, inda ya fara da rikicin dake wanzuwa tsakanin Isra'ila da Palestinawa wanda shi ne babban batu dake zama babbar barazanar tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China